‘Yan Kwadago Sun Yanke Matsaya a Kan Hakura da Zanga-Zanga Saboda Barazanar DSS

‘Yan Kwadago Sun Yanke Matsaya a Kan Hakura da Zanga-Zanga Saboda Barazanar DSS

  • Ma’aikatan Najeriya da ‘yan kasuwa a karkashin kungiyoyin kwadago dabam-dabam ba su fasa nunawa gwamnati takaicinsu ba
  • Takardun da aka samu daga kungiyoyi sun nuna sai sun ma’aikata fita zanga-zangar da NLC ta tsara a karshen watan Fubrairun nan
  • Gwamnatin Bola Tinubu da hukumar DSS A gefe guda sun yi gargadi a kan illar yi wa gwamnati zanga-zanga da sunan an shiga yunwa

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - ‘Yan kwadago sun sanar da cewa za su shirya zanga-zangar lumuna saboda kuncin rayuwa da yunwa da aka shiga a Najeriya.

Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu tayi bakin kokarinta na hana wannan zanga-zanga, amma bisa dukkan alamu har yau ba tayi nasara ba.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Matasa a Borno sun yi barazanar shiga Boko Haram, bayanai sun fito

Zanga-zanga
NLC: Zanga-zangar lumanar 'yan kwadago a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Bayanan da aka samu daga shafin NLC a dandalin X sun nuna babu abin da zai hana ma’aikatan da ke fadin kasar nan nuna takaicinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga-zangar lumanar NLC ta saba doka?

Shugabannin kungiyar NLC sun ce wannan aiki da suke shiryawa bai saba doka ba, kuma ba su nufin kawo tashin hankali da tarzoma.

Benson Upah ya ce sun tsara yadda za a fita zanga-zangar ba tare da an yi aika-aika ba.

Matsayar gwamnati a kan zanga-zanga

A rahoton Daily Trust, an ji cewa Ministan shari’a, Lateef Fagbemi ya ce taurin kan ‘yan kwadagon zai kai su ga yi wa kotu rashin kunya.

Fitattun lauyoyi kamar Femi Falana ba su yarda da maganar babban lauyan gwamnatin ba.

NLC ta sanar da masu shirin zanga-zanga

Kungiyoyin ma’aikatan gwamnati da irinsu AUPCTRE da ta ma’aikatan jiragen kasa duk sun tabbatar da cewa za su fita zanga-zangar.

Kara karanta wannan

Mata sun fito kan tituna zanga-zanga, sun aike da muhimmin saƙo ga ministan Tinubu

A madadin Sakararen kungiyar mawallafa da masu aikin dab’i a Najeriya, Azubuikwe Cnythia N. ta ce suna tare da 'yan NLC.

Shugabannin kungiyar NUJ ta ‘yan jarida da sakataren kungiyar NULGE, Isah Gambo sun nuna sun shirya shiga zanga-zangar lumanar.

Takardun da aka samu daga Abubakar V. Yusuf da Dominic Igwebike sun nuna ma’aikatan lantarki da ‘yan NAAT sun bi sahu.

Atiku ya ba Tinubu shawarwari

Rahoto ya zo cewa Atiku Abubakar ya fadawa Shugaba Tinubu dole a rage facaka da dukiya kuma a yi gwanjon kadarorin Najeriya.

Atiku Abubakar yake cewa Javier Milei ya ci karo da matsalar tsadar kaya, yawan bashi da talauci, amma ya kama hanyar gyara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel