Tsadar Rayuwa: Duk da Gargadin 'Yan Sanda, Mummunar Zanga-zanga Ta Barke a Legas, Bayanai Sun Fito
- Da safiyar yau Litinin ce 26 ga watan Faburairu aka barke da zanga-zanga a jihar Legas kan halin da ake ciki a kasar
- Zanga-zangar na zuwa ne bayan gargadin da kwamishinan 'yan sanda a jihar ya yi a jiya Lahadi 25 ga watan Faburairu
- hukumar kare hakkin dan Adam mai suna 'Take it Back Movement' ta fito zanga-zangar kan tsadar kayan abinci a Legas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Legas - Duk da barazana daga jami'an tsaro, jama'a sun barke da zanga-zangar don nuna damuwa kan halin da ake ciki a Legas.
Wata hukumar kare hakkin dan Adam 'Take it Back Movement' ta fito zanga-zangar kan tsadar kayan abinci a jihar Legas, cewar Punch.
Menene dalilin fitowa zanga-zangar a Legas?
Wannan na zuwa ne bayan jami'an tsaro sun yi gargadi kan fitowa zanga-zangar a fadin kasar duk da halin kunci da ake ciki, Daily Trust ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan 'yan sanda a jihar, Adegoke Fayoade a jiya Lahadi 25 ga watan Faburairu ya yi gargadi kan gudanar da zanga-zangar.
Masu zanga-zangar na rike da takardu da ke dauke da rubuce-rubuce na nuna rashin jin dadi kan tsadar kayayyaki, cewar The Nation.
An gano jami'an tsaro a wurin zanga-zangar
An gano jami'an 'yan sanda a wurin zanga-zangar don tabbatar da dakile tashin hankali a yayin gudanar da zanga-zangar.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan irin wannan zanga-zanga ta barke a jihar Neja da ke Arewacin Najeriya.
Daga bisani zanga-zangar ta sake fashewa a jihohin Kano da Oyo da kuma Cross River Kan tsadar rayuwa.
Zanga-zanga ta barke a Neja kan halin kunci
A baya, kun ji cewa Mazauna birnin Minna da ke jihar Neja sun fito zanga-zangar nuna rashin jin dadi kan tsadar rayuwa a kasar.
Mutanen sun fito zanga-zangar ce a ranar Litinin 5 ga watan Faburairu inda suka cika titunan birnin.
Wannan ya biyo bayan halin da 'yan kasar ke ciki na mawuyacin hali da matsin tattalin arziki.
Asali: Legit.ng