Kano: Abba Kabir Ya Gargadi Jami’an Wata Ma'aikata Kan Kula da Aiki, Ya Musu Babbar Barazana
- Jami’an SSO da aka dauka don kula da ingancin ilimi a jihar Kano sun sha gargadi daga gwamnati kan kula da aikinsu
- Gwamnatin jihar ta gargadi jami’an da ke kula da bangaren ilimi kan kula ayyukansu ko rasa alawus na su
- Kwamishinan ilimi a jihar, Umar Doguwa shi ya bayyana haka yayin wani taro da hadin gwiwar ma’aikatar ilimi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Gwamnatin jihar Kano ta gargadi jami’an da ke kula da bangaren ilimi, SSO kan kula ayyukansu ko rasa alawus.
Gwamnatin jihar ta yi barazana ga jami’an ne da cewa duk wanda karkashin kulawarsa aka samu nakasu a harkar ilimi zai fusknaci hukunci.
Wane gargadi gwamnatin Kano ta yi?
Kwamishinan ilimi a jihar, Umar Doguwa shi ya bayyana haka yayin wani taro da hadin gwiwar ma’aikatar ilimi, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Doguwa ya ce duk wani jami’ain da aka samu gazawa daga bangarensa zai iya rasa wani bangare na alawus na shi.
Kwamishinan wanda ya samu wakilcin daraktan tsare-tsare da bincike, Munzali Muhammad ya ce gwamnati ta himmatu wurin inganta fannin ilimi.
A cewarsa:
“Mun yi aiki kan wasu tsare-tsare guda hudu a Kano da suka hada da ilimin ‘ya’ya mata da tsare-tsaren malamai da tsare-tsaren jinsi da kuma masu kula da makarantu masu zaman kansu.
“Muna kira ga jami’an da ke kula da bangaren ilimin da su kula da makarantin da ke karkashinsu don samun abin da ake bukata.
“Zamu hukunta duk wadanda ake samun nakasu a bangarensu saboda muna ba su alawus a aikin da suke yi, zamu ki bai wa wadanda suka gaza alawus din saboda ana bai wa wadanda suka yi kokari ne.”
Martanin jami'in hukumar PLANE
Tun farko, shugaban hukumar PLANE, Umar Lawan ya ce wasu jami’an SSO da aka dauka sun gwammace su karbi aikin madadin koyarwa inda ko ba su yi aiki ba za a biya su.
Lawan ya ce wasu SSO din sun karanci yaren Arabiyya kuma an kai su wani bangare don kula da shi wanda dole a samu matsala dalilin haka.
Ya bukaci gwamnatin jihar ta dauki wasu tsauraran matakai don inganta harkar ilimi a fadin jihar baki daya, cewar BNN News.
Abba Kabir zai ciyar a watan Azumi
Kun ji cewa yayin da ake tunkarar watan azumin Ramadan, Abba Kabir zai taimakawa al'umma.
Gwamnatin jihar ta kafa kwamitin ciyar da mutane a azumin a fadin jihar musamman marasa karfi.
Asali: Legit.ng