Dakarun Sojoji Sun Sake Kashe Bakaken Shugabannin ‘Yan Bindiga da Yaransu

Dakarun Sojoji Sun Sake Kashe Bakaken Shugabannin ‘Yan Bindiga da Yaransu

Gawurtattun ‘yan bindigan da ke barna a jihohi Arewa sun bakunci lahira a sakamakon wasu hare-haren sojojin Najeriya

Sojoji sun kashe Baldo da Baban Yara da kuma wasu yaransu da aka yi barin wuta a yankin Aliero da ke jihar Kebbi a Arewa ta yamma

Jami’an tsaro suna kokarin kauda duk wasu miyagu domin mutanen kauyuka su iya yin noma da kyau a shekarar nan da aka shiga

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Zamfara - Kwanaki kadan bayan mutuwar Boderi, sai aka samu labari cewa an yi nasarar hallaka wasu ‘yan bindiga a Najeriya.

Rahoton PR Nigeria ya tabbatar da cewa rundunar sojojin Najeriya ta kashe Baldo da Baban Yara da ke yankin Katsina da Zamfara.

Kara karanta wannan

Tattalin arziki: Abin da Tinubu ya fadawa Dangote, Elumelu, BUA da aka hadu a Aso Villa

Sojoji
Sojoji sun casa 'yan bindiga a Aliero Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun mutu a jeji

Wadannan miyagu suna cikin wadanda ake zargi sun addabi mutanen Arewa ta yamma.

Wata majiya ta ce a ranar Asabar da ta gabata aka kashe wadannan jagororin ‘yan bindiga a tsakanin jihohin Katsina da Zamfara.

Kafin rasuwarsu, Baldo da Baban Yara sun taka rawar gani sosai wajen dauke mutanen da aka yi garkuwa da su a cikin jeji.

Ana so a murkushe 'ya bindiga

An rahoto cewa wani jami’in soja ya tabbatar da suna kai hare-hare domin ganin bayan ‘yan bindigan da ke faman ta’adi a Arewa.

"Dakarunmu sun gwabza da ‘yan ta’adda a yammacin Aliero kuma sun yi nasarar kashe jagororin ‘yan bindiga da mayakansu 28."

"A baya-bayan nan, rundunarmu sun huro wuta wajen kai hare-hare a Arewa maso yamma kuma suna yin kaca-kaca da ‘yan ta’adda."

Kara karanta wannan

Bayan jami'an sun kashe shugabannin 'yan bindiga, tsageru sun afkawa mutane a Kaduna

- Wani jami'in soja

Za a samu isasshen abinci a 2024?

Abin da sojoji suke so shi ne kawo karshen ‘yan bindiga ta yadda manoma za su iya fara shirin yin noma sosai a shekarar nan.

Rashin noma a garuruwa zai haifar da karancin abinci, tsada da karin matsin tattalin arziki.

'Yan bindiga suna ganin haza a jeji

Wani ‘dan sa kai da ya zanta da jaridar, ya ce babu wani ‘dan ta’adda da ake raga masa, sojoji suna fatattakar miyagun da aka gani.

Jami’an sojojin suna aiki da bayanan sirri, da zarar sun ji labarin ‘yan bindiga, sai su shiga duk inda suke domin su hallaka su nan-take.

Fayose ya soki mulkin Buhari

A bangaren tattalin arziki, ana da labari Ayo Fayose yana ganin mulkin Muhammadu Buhari na shekaru takwas ba alheri ya zama ba.

Tsohon gwamnan ya ce mushen tattalin arziki aka mikawa Bola Tinubu kuma babu abin da zai iya domin ya gaji biyan bashin da aka ci.

Kara karanta wannan

Babban abin kunya: An kama matashi da laifin sace motar surukinsa, ya siyar N230,000

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng