Tattalin Arziki: Abin da Tinubu Ya Fadawa Dangote, Elumelu, BUA da Aka Hadu a Aso Villa
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kira manyan ‘yan kasuwan da ake ji da su domin ganin an farfado da tattalin arzikin Najeriya
- Aliko Dangote, Abdussamad Rabiu da Tony Elumelu suna cikin wadanda aka sa labule da su ranar Lahadi a fadar Aso Rock Villa
- Ana neman yadda ‘yan kasuwan za su iya taimakawa gwamnati a samu isasshen abinci, ayyukan yi sannan Naira tayi daraja
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - A yammacin Lahadi, Bola Ahmed Tinubu ya yi zama da manyan ‘yan kasuwa kan matsalar tattalin arziki da ake fuskanta a yau.
Wasu gwamnonin jihohi sun samu halartar wannan muhimmin zama da aka yi a Abuja kamar yadda Premium Times ta fitar da rahoto.
Attajirai da 'yan kasuwa sun hada da Tinubu
‘Yan kasuwan da aka kebe da su sun hada da shugaban Dangote Group, Aliko Dangote.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wajen tattaunawar akwai Abdulsamad Rabiu wanda shi ne shugaban kamfanin BUA da shugaban bankin UBA, Tony Elumelu.
Darekta Janar na kungiyar MAN, Segun Ajayi-Kadir ya samu halartar zaman na jiya.
Gwamnonin jihohi a taron tattalin arziki
A bangaren gwamnoni akwai Dapo Abiodun da Farfesa Charles Chukweuma Soludo wanda ya taba yin gwamnan babban bankin CBN.
Shugaban Najeriyan ya nemi a ba shi shawarar yadda zai farfado da tattalin arzikin kasar, ya ce gwamnatinsa za ta rika karbar shawara.
Rahoton ya ce Bola Tinubu ya fadawa ’yan kasuwar ya tara su ne domin duba halin tattalin da aka shiga da irin kokarin da yake yi.
Baya ga dabarun da gwamnatinsa ta fito da su, Tinubu ya ce kofarsa a bude ta ke domin ganin an faranta ran al’umma a mulkinsa.
Abin da Tinubu ya fadawa Dangote da sauransu
Da aka zanta da su bayan taron, Aliko Dangote ya ce sun tattauna ne a kan yadda za a samar da abinci sannan a iya kirkiro da ayyukan yi.
Mai kudin Afrikan bai fadi dalla-dallar abin da aka zanta ba, amma ya nuna inda aka dosa, Abdussamad Rabiu ne ya yi zancen tashin Dala.
Shugaban BUA ya nuna yadda Naira ta ke karyewa ba zahirin gaskiyar yadda kasuwa ta ke tafiya ba ne, ya kuma yabi hobbasan CBN.
Tony Elumelu ya yi bayani kan yadda za a rage talauci yayin da Ajayi-Kadir ya ce za su dabbaka matakan da gwamnatin kasar ta dauka.
Halin tattalin aarziki ya kai NLC ga zanga-zanga
Duk da gargadin gwamnatin tarayya, ana da labari shugabannin kwadago sun ki hakura da zanga-zanga saboda matsin da aka shiga.
‘Yan jarida, ma’aikatan lantarki, masu aiki a jiragen kasa da ‘yan kungiyar mawallafa sun ki sauraron gargadin DSS da na Ministan shari’a.
Asali: Legit.ng