Abubuwan da ya kamata ka sani a kan AbdulSamad Rabiu yayin da ya cika 60

Abubuwan da ya kamata ka sani a kan AbdulSamad Rabiu yayin da ya cika 60

A yau Laraba, 4 ga watan Agusta, 2020 ne Abdul Samad Rabiu ya cika shekaru 60 a Duniya. Shugaba Buhari da Atiku Abubakar duk sun fito sun taya shi murna.

A jerin Attajiran Duniya ta mujallar Forbes ta fitar a 2020, masu kudin Najeriya hudu ne kacal su ka samu shiga, daga cikinsu har da shi Alhaji Abdul Samad Rabiu.

Ko da cewa Aliko Dangote da Mike Adenuga sun rike matsayinsu a sahun masu kudin Najeriya, dukiyar Abdul Samad Rabiu wanda ya kutso kai daga baya, gaba ta ke yi.

A ‘yan shekarun bayan nan, shugaban kamfanin na BUA ya ribanya arzikinsa, inda yanzu mujallar Forbes ta ke yi masa hasashen ya ba fam Dala biliyan 3.18 baya.

Da wannan tarin dukiya, Alhaji Rabiu ne na uku a masu kudin Najeriya, kuma na takwas a Nahiyar Afrika. Kuma ya na cikin sahun Attajirai 2, 000 da ake da su a Duniya.

Rabiu ya kafa kamfaninsa na BUA ne a 1988, yanzu wannan kamfani hade da sabon kamfanin simintin Obu ya na da hannun jari na fiye da Naira tiriliyan 1.18 a Najeriya.

KU KARANTA: Dukiyar Abdul Samad Rabiu ta karu da $650m a shekara 1

Abubuwan da ya kamata ka sani a kan AbdulSamad Rabiu yayin da ya cika 60
AbdulSamad Isiyaka Rabiu
Asali: Twitter

Bayan sumunti, attajirin ya shiga harkar kasuwancin sukari, safarar kaya daga ketare, gidaje, kayan gona, man gyada, shigo da shinkafa, fulawa da kuma kayan karafuna.

Kamar yadda Nairametrics ta bayyana, Rabiu ya taso ne bai da komai, amma yanzu kamfaninsa ya na samun rarar dala biliyan 2.5 duk shekara, kuma sunansa ya ratsa ko ina.

A shekarun baya Rabiu ya saye kamfanin Nigerian Oil Mills LTD. A 2008 ne kuma kamfanin BUA su ka yi karfi a harkar sukari, wanda a da sunanDangote kawai ake ji a Najeriya.

Bayan ya gamu da jarrabawa a shekarun baya, mai kamfanin na BUA ya dawo da karfinsa a 2013 da kimanin Dala biliyan 1 aljihunsa, dukiyar da yanzu ya nunka ta kusan uku.

Mahaifin Abdul Samad Rabiu shi ne shararren malamin nan kuma ‘dan kasuwa da aka yi a Kano, Marigayi Sheikh Isyaka Rabiu. Kamar mahaifinsa, shi ma ya na taimakon al’umma.

AbdulSamad Rabiu ya na da ‘yanuwa fiye da 40 wurin mahaifinsa, shi ma ya na da ‘ya ya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel