Dan Najeriya Ya Burge Jama’a Yayin da Ya Kama Sana’ar Aski a Turai, an Yaba da Kwarewarsa

Dan Najeriya Ya Burge Jama’a Yayin da Ya Kama Sana’ar Aski a Turai, an Yaba da Kwarewarsa

  • Bidiyon wani mai sana’ar aski dan Najeriya da ya koma kasar Canada kuma yake burge abokan huldarsa da kayatar da jama’a a kafar sada zumunta
  • Daifan bidiyon ya nuna ma’askin yana yin gyaran fuska ga wani abokin huldarsa wanda ke zaune don a yi masa aski a natse
  • Abokin huldar ya bayyana yana farin ciki da askin da aka masa, wanda ya nuna basirar ma’askin da fikirar da yake da iya

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Wani mai sana’ar aski dan Najeriya da ya koma kasar Canada ya baiwa kwastomominsa mamaki da kalan askin da ya iya mai ban mamaki, ya kuma burge jama’a a TikTok.

Kara karanta wannan

Matashi ya tafka kuskure, ya tankado katin waya na N35k a madadin na N3500 daga bankinsa

An yada bidiyon askin nasa a kafar TikTok, inda ya sami dubban dangwale da nuna sha’awar dubban jama’a.

Matashi ya kama aski a Canada bayan hijira daga Najeriya
Yadda dan Najeriya ya kama sana'ar aski a Canada | Hoto: @iroko_bass1/TikTok
Asali: TikTok

Bidiyon ya dauki lokacin da ma’askin ke yiwa wani abokin huldarsa aski, inda aka ga yana cancara masa gyaran fuska mai kyau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwastomominsa sun nuna sha’awar askinsa

Abokin huldar ya zauna hankali kwance a kujerar ma’askin, ya nuna natsuwar a yi masa gyaran fuskar da zai burge mutane.

Alamu sun nuna wanda ake yiwa askin na cikin farin ciki da sabon salon askin da aka masa, wanda ya bayyana yabo ga basira da fikirar ma’askin.

Bidiyon, kamar yadda @iroko_bass1 ya yada, ya kuma burge da yawan masu amfani da TikTok, wadanda suka yaba da salon askin da kuma kwarewar matashin.

Kalli bidiyon a kasa:

Yadda ‘yan Najeriya ke fecewa kasashen waje

Idan muka waiwaya baya kadan, za ku ga yadda ‘yan Najeriya ke yawan fita daga Najeriya zuwa kasashen waje.

Kara karanta wannan

Bayan jami'an sun kashe shugabannin 'yan bindiga, tsageru sun afkawa mutane a Kaduna

Wannan dai na da nasaba ne da yadda ‘yan kasar ke hijira don neman hanyoyin samun abin da za su rike kansu.

Hakazalika, tattalin arzikin Najeriya na daga cikin dalilan da ke koran ‘yan kasar zuwa kasashen waje.

Matashi ya siya katin N35k cikin kuskure a Najeriya

A bangare guda, kun ji yadda wani matashi dan Najeriya ya tafka kuskuren siyan katin waya daga banki fiye da yadda yake bukata.

An ga bidiyon yadda matashin ya nuna shaidar siyan katin N35,000 a yanayin da ake ciki a kasar nan na koma bayan tattalin arziki.

A yadda yace, ya yi niyyar siyan katin N3500 ne, amma haka ya kuskure. Jama’a a kafar sada zumunta sun ba shi shawarin yadda zai yi da katin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.