Matashi Ya Tafka Kuskure, Ya Tankado Katin Waya Na N35k a Madadin Na N3500 Daga Bankinsa

Matashi Ya Tafka Kuskure, Ya Tankado Katin Waya Na N35k a Madadin Na N3500 Daga Bankinsa

  • Wani dan Najeriya ya yi kuskuren danna N35,000 a madadin N3500 a matsayin katin waya da ya yi niyyar siya ta banki
  • A wani bidiyon da ya yadu a kafar sada zumunta, matashin ya nuna sakon da aka tura masa na shaidar siyan katin na MTN
  • Hakazalika, ya bayyana yadda ya yi kuskuren siyan katin daga bankinsa na Zenith, lamarin da ya dauki hankali

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

A wani bidiyon da ya yadu a kafar sada zumunta, wani matashi dan Najeriya ya bayyana babban kuskuren da ya yi na siyan katin N35,000 a madadin N3500 daga bankinsa.

A madadin ya latsa N3500, sai kawai ya sanya N350,000 wanda daga nan aka tura masa katinsa daga banki.

Kara karanta wannan

Hazikin matashi ya kera otal da katafaren gida daga kwalaye, bisararsa ta burge mutane

Matashin dai ya shiga tashin hankali, inda ya zo kafar sada zumunta tare da nunawa duniya irin kuskuren da ya tafka a bankinsa na Zenith.

Matashi ya shiga mamaki bayan siyan katin N35000
Yadda matashi ya siya kati mai tsada ta banki | An yi amfani da hoton nan ne a matsayin gwada misalin shiga damuwa
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya dauki bidiyo tare da yada shaidar siyan katin a kafar TikTok mai suna @blackieee.

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin jama’a ga bidiyon siyan katin waya na N35,000

Bayan yaduwar bidiyon a kafar sada zumunta, Legit ta tattaro kadan daga abin da jama’a ke cewa kan wannan bidiyo mai ban dariya da ban tausayi da dariya.

D3vmo:

“To kai har kana da 35k? Wa ka kashe?”

Sochi:

“Rashin isasshen kudi zai cece ni a nan.”

Adesola:

“Zan siya 30k idan MTN ne.”

Blessingblack08:

“Tabbas MTN ne zo ka yi kawai.”

Gen:

“Ka siyarwa PalmPay ta hanyar juya katin zuwa kudi.”

Sharon:

“Akalla ba ka ma yi kuskuren turawa wata lambar ba.”

Kara karanta wannan

"Ba ta siyarwa bace": Uba ya mayarwa ango da kudin sadakin diyarsa, ya yi magana 1 mai ratsa zuciya

Chommy Global 1:

“Ka siyarwa mutane 10 a nan sai ka fada min nawa kudin.”

GoodbhadbovyyA:

“Wannan yasa nake son UBA... ba za ka iya siyan katin da ya wuce na 5k ba.”

DICENATION:

“Akwai mutane da yawa da rashin isasshen kudi zai taimake su a nan.”

Patienceasuquo961:

“Har ma kana da hanyar siyan katin 3500 yanzu ka san inda ka sa kanka.”

Jihohin Najeriya da aka fi amfani da intanet

A wani rahotonmu na baya, kunji yadda muka tattaro muku jerin jihohi 10 da ‘yan Najeriya suka fi amfani da intanet.

Wannan na zuwa ne daga wani rahoton da NBS ta fitar mai alhakin tattara bayanai kan kusan komai a Najeriya.

An bayyana jihohin Kano, Kaduna da Legas daga jihohin da aka fi samun masu amfani da intanet.

Asali: Legit.ng

Online view pixel