Mijin Hajiya: Bidiyon Mutumin da Ya Goyi Dansa Suka Shiga Kasuwa Ya Jawo Cece-Kuce a Duniya

Mijin Hajiya: Bidiyon Mutumin da Ya Goyi Dansa Suka Shiga Kasuwa Ya Jawo Cece-Kuce a Duniya

  • An hangi wani mutum a wata babbar kasuwa da wani karamin jariri daure a bayansa kamar yadda mata ke yi
  • An ga mutumin ne a lokacin da yake siyan kayan lambu, mutane sun kasa daurewa sai kallonsa suke cikin mamaki
  • Bayan da aka yada bidiyon a kafar TikTok, mutane da yawa sun yabawa mutumin saboda basirar renon yara da yake dashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Najeriya - Wani faifan bidiyo mai sosa rai ya nuna yadda wani dan Najeriya ya burge jama'a a kasuwa ta hanyar goyon jariri yana yawo a kasuwa.

A cikin bidiyon da Ade Jennifer ta raba a TikTok, mutumin ya zo kasuwa ne don siyan kayan lambu, kamar yadda aka gani.

Kara karanta wannan

Matashi ya kawata adaidaita sahunsa ta koma tamkar Marsandi, bidiyon ya girgiza intanet

Bidiyon mijin da aka gano yana goyon jariri
Mijin hajiya ya goyi jariri a kasuwa | Hoto: TikTok/@adajennifer9.
Asali: TikTok

Mutane sun yi sha'awar shi saboda jaririn da ke bayansa, inda kuma Jennifer ta yi amfani da wayarta don daukar bidiyonsa da yaron da ke bayansa tare da nunawa duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka dauki bidiyonsa

Jennifer ta bayyana mutumin a matsayin miji na-gari saboda yadda yake tallafawa matarsa wajen renon jaririn.

Wannan bidiyon dai ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta, mutane da yawa sun bayyana ra'ayoyinsu game da wannan.

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a

@ifeomaugochukwu858:

"Ranar da na yi tafiya zuwa neman aiki, mijina ya so ya kashe ni da kira."

@AsaAbig:

"Allah ya kara maka nisan kwana ranka ya dade, amin dan uwa. Ya yi kyau, ka ci gaba da yi."

@fleta:

"Wani yayi sauri ya fada ma iyayensa, matarsa ta mallake shi, babu abinda zaku fada min."

@Frank:

"Mene ne abu mai kyau a cikin wannan? Tafi ka yi harkallarka ka turo kudi don yi maka irin wannan aikin."

Kara karanta wannan

"Zai hadiye cokali": Bidiyon wani dan Najeriya a gidan abinci ya girgiza intanet

@Technician:

"Talaka ya auri attajira."

@temi:

"Ina sonka sosai, mijina ya kamata ya koya wannan."

@Azubuike okonkwo Iwuba:

"Asiri na aiki."

@vivilove:

"Ya kamata mijina ya gwada wannan."

@Nelson Daniels338:

"Amma don kada matar ta ta yi sakaci da saukin kan wannan mijin saboda na san me nake fadi."

Ba zan maimaita kuskuren iyayena

A wani labarin, matashiya 'yar Najeriya da ke aikin podcast ta sha alwashin auren mai kudi ko ta halin kaka, a cewar ta ba za ta aikata kuskuren da iyayenta suka yi ba.

Matashiyar mai suna Pearl, a shirin podcast na 'yan sama da shekaru 18, ta ce soyayya ba za ta rude ta wajen auren mutum don asalinsa ba, kudi kawai za ta bi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel