Ma’aurata Sun Koka Yayin da Mutane Suka Ki Halartan Bikinsu Bayan Sun Kashe Miliyan 43, Bidiyo

Ma’aurata Sun Koka Yayin da Mutane Suka Ki Halartan Bikinsu Bayan Sun Kashe Miliyan 43, Bidiyo

  • Gabannin bikinsu, wasu ma'aurata sun aika katin gayyata ga mutane kuma 88 daga ciki sun tabbatar da za su halarci taron bikin
  • Sai dai kuma, sun gano babu ko mutum daya da ya hallara don halartan bikin aurensu, bayan sun kashe makudan kudade
  • Wani bidiyo da ke nuna dakin taron wanda ke cike da kujeru da taburan da aka tanada don baki ya karya zukatan mutane da dama

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wasu ma'aurata sun shiga mawuyacin hali bayan bakin da suka gayyata don halartan shagalin bikinsu sun ki amsa gayyata.

Daily Mail ta rahoto cewa ma'auratan sun kashe sama da dala 27,000 (fiye da naira miliyan 43) kan bikin kuma sun samu tabbaci daga mutum 88.

Kara karanta wannan

Halin kunci: Yan Najeriya sun sako jarumar fim a gaba kan kamfen a zabi Tinubu, ta shiga damuwa

Babu ko mutum daya da ya halarci bikin
An yi amfani da hoton don misali ne: Hoto: Jasmin Merdan, TikTok/@grayanxiety
Asali: Getty Images

Daya daga cikin ma'auratan, @grayanxiety, ya yada wani bidiyo a TikTok yana nuna dakin taron babu kowa cike da teburan da aka tanada saboda baki amma suka ki hallara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mutum 88 sun amsa da eh...amma ko 40 basu zo ba," taken da aka yi wa bidiyon.

Bidiyon ya samu mutum fiye da miliyan biyar da suka kalla a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Yayin da lamarin ma'auratan ya zama mai karya zuciya, wata amarya ta samu kanta cikin yanayi makamancin wannan.

Kalli bidiyon a kasa:

Mutane sun tausayawa ma'auratan

Viintagepearlsss ta ce:

"Mutane uku ne kawai suka hallara a nawa. 97% na bakinmu 'yan uwan mijina ne."

johnhinkelman246 ya ce:

"Idan mutane suka nuna maka ainahin dabi'unsu, ka yarda da su a karon farko - Maya Angelou."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun toshe fitaccen titi a Arewacin Najeriya, sun sace matafiya masu ɗumbin Yawa

zachwight999 ya ce:

"Abin da ke faruwa da ni a kodayaushe kun san abincin liyafa nawa na zubar."

ermrphy ya ce:

"Na yi mai kida a wani biki haka. Na tausayawa amaryar, tana ta kuka, sun ce sun tabbatar da zuwan mutum 120 kuma kimanin 15 ne kawai suka hallara."

Vindeg ya ce:

"Abun bakin ciki ne...amma dai akalla ba sai kin yi masu wani abu bna kuma."

Ma'aurata sun kama masu rabon abinci

A wani labarin kuma, mun ji cewa an shiga rudani a wajen wani biki yayin da aka kama wata mai rabon abinci da laifin satar abincin da ma'auratan suka siya don rabawa baki.

A cewar @favour_gist, mai rabon abincin ta hana bakin da aka ce ta kaiwa, ta boye da zummar guduwa da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng