An Tanadi Buhuna 985,044 Za a Rabawa Talakawa Abinci Inji Fadar Shugaban Kasa
- Fadar shugaban kasa ta yi karin haske a kan inda aka kwana a alkawarin rabon kayan abinci ga marasa karfi a kowace jiha
- Jawabin da Bayo Onanuga ya fitar ya tabbatar da cewa an tanadi metric 42, 000 a cikin 102, 000, za a fara rabawa marasa hali
- Hadimin shugaban Najeriyan ya yi bayanin abin da ya sa aka ji shiru tun bayan alkawarin da aka dauka a farkon Fubrairun nan
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
FCT, Abuja - A ranar Juma’ar nan fadar shugaban kasa ta sanar da inda aka kwana game da alkawarin raba metric ton 42, 000 na hatsi.
Mai taimakawa shugaban kasa wajen yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya sanar da wannan a wani jawabi da ya fitar a Aso Villa.
Gwamnati za tayi rabon abinci
Mista Bayo Onanuga ya yi wa jawabin taken ‘Inda aka kwana a kokarin gwamnatin Bola Tinubu na samar da abinci a kasar nan.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwanakin baya aka rahoto gwamnatin tarayya ta ce za a fito da metric ton 102,000 na hatsi da za a rabawa wadanda ke cikin bukata.
Hadimin shugaban kasar ya ce gwamnatin tarayya ta bi ta hannun ma’aikatar noma da samar da abinci domin a raba buhunan hatsin.
Yadda za a bi wajen raba buhunan hatsi
Onanuga yake cewa wadanda za a ba kayan abincin su ne marasa galihu a fadin kasar, Sanarwar ta ce hukumar NEMA za tayi rabon.
Za a sayo ragowar metric ton 60, 000 a kasuwa a hannun kamfanonin shinkafa.
“Hatsin suna muhimman wuraren ajiya bakwai, yanzu ana dura su a buhu domin mika su ga hukumar NEMA mai bada agajin gaggawa.”
“Bukatar a zuba hatsin a cikin buhu ya jawo aka bata lokaci domin sai da gwamnatin tarayya ta bada sabuwar kwangilar buhunan.”
- Bayo Onanuga
Za a samu abinci daga noman rani
Ba a nan kadai jawabin Onanuga ya tsaya ba, hadimin ya ce tun Nuwamba aka fara shirin aikin noman alkama da rani a wasu jihohi.
Nan da ‘yan makonni kadan za a girbe noman da aka yi sannan za a sake yin sahu na biyu na shukan a tsarin noman ranin da ake yi.
Za a noma shinkafa, rogo da masara inda gwamnati ta ke bada tallafi a tsarin NAGS-AP da gwamnatin Jigawa ta dage a kan aikin.
Farashin abincin zai tashi a kasuwa?
Domin cike gibin da ake nema, gwamnatin tarayya za ta sayo metric ton 60, 000 a kasuwa, Legit ji ta-cewar masana tattalin arziki.
Idan za a nemo abincin ne a hannun manoman da ke neman kudi domin damina, Dr. Usman Bello ya ce watakila farashin hatsi ya tashi.
Malamin jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya yake cewa kamfanoni da manyan ‘yan kasuwa za su saidawa gwamnati kayan da daraja.
A karshe za a samu abinci da za a ci
Sai da aka shafe makonni biyu, gwamnatin Bola Tinubu ba ta waiwayi wannan alkawari ba. A cikin makon nan aka fitar da rahoton.
Da aka tuntubi jami’an hukumar NEMA da ma’aikatar noma, an tabbatar da cewa har zuwa lokacin, kayan da za a raba ba su iso ba tukun.
Asali: Legit.ng