EFCC Ta Bankado Dala Miliyan 800 Daga Gidan Tsohon Gwamnan PDP? Gaskiya Ta Bayyana

EFCC Ta Bankado Dala Miliyan 800 Daga Gidan Tsohon Gwamnan PDP? Gaskiya Ta Bayyana

  • An yi wani ikirari a soshiyal midiya a watan Fabrairu cewa EFCC ta bankado damin kudi dala miliyan 800 a gidan tsohon gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu
  • Wadanda suka wallafa labarin sun yi ikirarin cewa wasu jami'an EFCC sun farmaki gidan tsohon gwamnan jihar Abia kuma sun gano makudan kudade 'yan kasar waje
  • Sai dai kuma, wani binciken gaskiya ya ce wallafan kanzon kurege ne kuma bai nuna kudin da aka gano a gidan Ikpeazu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Umuahia, jihar Abia - Wani hoto ya yi ikirarin cewa jami'an hukumar EFCC sun gano damin kudi a gidan tsohon gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu.

Wadanda ke yada labarin sun yi zargin cewa kudaden da aka gano a gidan Ikpeazu ya kai dala miliyan 800.

Kara karanta wannan

Yadda aka bi har gida aka kashe wata uwa tare da raunata 'diyarta a jihar Arewa

Ikpeazu ya kasance babban jigo ne a jam'iyyar PDP kuma tsohon gwamnan jihar Abia sau biyu.

Bincike ya nuna EFCC bata kai samame gidan Ikpeazu ba
EFCC Ta Bankado Dala Miliyan 800 Daga Gidan Tsohon Gwamnan PDP? Gaskiya Ta Bayyana Hoto: @IkpeazuOkezie, @officialEFCC, @VusiSambo
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A daya bangaren, EFCC hukuma ce da ke binciken masu aikata laifukan da suka shafin cin hanci da rashawa.

Labarin na Ikpeazu ya yadu a shafin Facebook, sannan an hada shi da hoton damin kudi. An kuma gano labarin a dandalin X (wanda aka fi sani da Twitter a baya).

Daya daga cikin irin labaran na cewa:

"Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gano damin kudi dala miliyan 800 a gidan tsohon gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu."

Ana iya ganin ikirarin kan Facebook a nan da nan.

Ikirarin cewa EFCC ta farmaki gidan Ikpeazu karya ne

Amma shin ikirarin gaskiya ne? Wani dandalin binciken gaskiya, Africa Check, ya gudanar da bincike.

Kara karanta wannan

Jami’an EFCC sun kai samame wurin ‘yan canji a Kano, Abuja da Oyo akan wani dalili 1 tak

Bayan binciken da aka yi, dandalin ya ce hoton ya fito ne daga wani samame da aka kai a kasar Mexico.

Ya kara da cewar hoton na yawo a dandalin soshiyal midiya tun a shekarar 2007 kuma bai nuna damin kudin da aka gano a gidan tsohon gwamnan Abia.

Bugu da kari, Africa Check ta ce idan aka yi la'akari da matsayin Ikpeazu a Najeriya, datuni labarin gano irin wannan makudan kudi a gidansa zai yadu a kafafen watsa labarai.

EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan Kwara

A gefe guda, mun ji cewa hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatahi Ahmed a gaban kotu.

Kamar yadda Channels tv ta tattaro, EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan ne a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Ilorin ranar Jumu'a, 23 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng