"Ina Ji a Jika": Tsohon Gwamna Ya Koka Kan Daurin da EFCC Ta Yi Masa

"Ina Ji a Jika": Tsohon Gwamna Ya Koka Kan Daurin da EFCC Ta Yi Masa

  • Tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, ya koka kan hana shi ganin likitansa, samun magunguna da mai dafa masa abinci
  • Ahmed yana zargin hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) da hana shi beli bayan ya cika sharuɗɗan da ta gindaya
  • Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa na yiwa Ahmed tambayoyi kan wasu maƙudan kudade na biliyoyin naira a lokacin da yake gwamnan jihar Kwara

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ilorin, jihar Kwara - Tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, ya zargi hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC da ci gaba da tsare shi duk da cika dukkan sharuddan belinsa ba tare da wani dalili ba.

Kara karanta wannan

EFCC ta tsare tsohon gwamnan Arewa tsawon kwanaki 2 kan wawushe N10bn, ta ɗauki mataki 1

Kamar yadda tashar talabijin ta Arise TV ta ruwaito, mai magana da yawun Ahmed Abdulwahab Oba, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a daren ranar Talata, 20 ga watan Fabrairu.

Abdulfatah Ahmed ya koka a hannun EFCC
EFCC dai na bincikar tsohon gwamnan kan badakalar wasu makudan kudade Hoto: @officialEFCC/@AbdulfataAhmed
Asali: Twitter

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Bugu da ƙari, an hana shi samun damar zuwa ga likitocinsa, samun magunguna da samun damar ganin mai dafa abincinsa kai tsaye".

Ya buƙaci hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa da ta bi ƙa’idojin da suka dace don ganin sun nuna gaskiya wajen tafiyar da lamarin.

Menene ƙorafin Abdulfatah kan EFCC?

Kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito, Oba ya bayyana cewa bai taɓa ƙin amsa dukkan gayyata da hukumar ta yi masa a baya ba, inda ya bayyana cewa an mayar da shari’ar zuwa Ilọrin, babban birnin jihar Kwara daga ofishin EFCC da ke Abuja kan batun shari’a.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Kashim Shettima Ya Fadi Abu 1 da Tinubu ke yi wanda zai faranta ran 'yan Najeriya

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

"Eh, har yanzu yana tare da EFCC kuma a yanzu muna cikin ruɗani game da batun saboda suna ci gaba da canza raga a lokacin wasan.
Shari'ar tana ɗaukar sabon salo wanda a gaskiya yanzu ba mu fahimta.
"Da farko sun ce suna son ya kawo masu tsaya masa guda biyu waɗanda daraktoci ne a matakin tarayya.
"Waɗanda za su tsaya masu sun zo sai kuma aka buƙaci mu kawo kadarorin a Abuja. Muna ganin wannan a matsayin saɓani."

Zargin Emefiele Ya Sa Akpabio a Matsala

A wani labarin kuma, kun ji cewa zargin lalata tattalin arziƙin ƙasar nan da Godswill Akpabio, ya yi wa Godwin Emefiele, ya sanya shi cikin matsala.

Godwin Emefiele ya yi barazanar maka shugaban majalisar dattawan a gaban kotu saboda a ganinsa yana ƙoƙarin ɓata masa suna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel