Tsadar Rayuwa: Babbar Matsalar Tinubu Gwamnoni Ne, Kungiya Ta Fadi Abin da Gwamnonin Ke Yi a Boye
- An zargi gwamnonin jihohin Najeriya da kawo cikas a tsare-tsaren Shugaba Tinubu musamman a wannan yanayi da ake ciki
- Wata Kungiyar ta ce gwamnonin ke dakile shirin shugaban wurin inganta tattalin arzikin kasar don ganin ya tsaya da kafafunsa
- Legit Hausa ta ji ta bakin wani malami kuma masanin tattalin arziki a Gombe kan zargin gwamnonin da ake yi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Wata kungiyar kare al’umma a Najeriya ta zargi gwamnonin jihohi da kawo cikas a kokarin Tinubu na kawo sauyi a kasar.
Kungiyar ta ce gwamnonin ke dakile shirin shugaban wurin inganta tattalin arzikin kasar ya tsaya da kafafunsa.
Menen kungiyar ke zargin gwamnonin?
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a Abuja a jiya Alhamis 22 ga watan Faburairu, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kungiyar, Dakta Godwin Abutu ya zargi gwamnonin da alkawarin iska musamman a halin da ake ciki, People Daily ta tattaro.
A cewarsa:
“Dukkanmu mun yi ta kiran a cire tallafin mai a kasar, ganin yanzu an cire dole mu tsaya mu tabbatar da hakan."
Sun bayyana babbar matsalar gwamnonin
Ta kara da cewa:
“Babbar matsalar gwamnonin ita ce madadin su yi amfani da tsarin wurin kawo ci gaba a yankunansu amma sai suke kara lalata lamarin wurin rike albashin ma’aikata.
“A jiya mun ji cewa shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya ce an bai wa ko wane gwamna biliyan 30 don karya farashin kaya, amma har yanzu ba mu ji komai daga gare su ba.”
Kungiyar har ila yau, ta ce ana iya tuna a watan Disambar 2023 an ba da kayan abinci amma sai suka rarraba kayan ga wadanda suka sani ba tare da mabukata sun samu ba.
Legit Hausa ta ji ta bakin wani malami kuma masanin tattalin arziki a Gombe:
Muhammad Lamido ya ce tabbas idan ana auna bunkasar tattalin arziki daga jihohi ya ke durkushewa.
Ya ce:
"Dukkan alamu sun tabbatar da cewa gwamnonin na daga cikin wadanda ke jawo matsala a kasar.
"Tun lokacin Buhari game da kudaden kananan hukumomi har zuwa kayan rage radadin cire tallafi sun taka rawa wurin jefa al'umma halin matsi."
Matasa sun yi barazana a Borno
Kun ji cewa wasu matasa sun fito zanga-zanga a jihar Borno tare da yin barazana ga gwamnati kan halin kunci da ake ciki.
Matasan da suka gudanar da zanga-zangar a garin Dikwa da ke jihar sun yi barazanar shiga kungiyar Boko Haram idan ba a dauki mataki ba.
Wannan na zuwa ne yayin da ‘yan Najeriya ke cikin mawuyacin halin kuncin rayuwa da tsadar kayayyaki.
Asali: Legit.ng