Akpabio: Karya Ake Yi, Gwamnati Ba Ta Raba Mana N30bn ba - Gwamnonin APC da PDP

Akpabio: Karya Ake Yi, Gwamnati Ba Ta Raba Mana N30bn ba - Gwamnonin APC da PDP

  • Godswill Akpabio ya yi ikirarin kowane gwamna ya samu karin N30bn baya ga kudin da aka saba ba jihohi a duk karshen wata
  • Abin mamaki sai aka ji gwamnatoci da yawa sun musanya maganar, sun ce babu kudin da aka aiko masu domin magance yunwa
  • Gwamnatocin Benuwai, Osun, Katsina da na Legas suna cikin wadanda suka karyata maganar da Sanata Akpbabio ya yi a fili

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A ranar Alhamis wasu gwamnatocin jihohi suka karyata maganar kudin da Godswill Akpabio ya yi a zauren majalisar dattawa.

Punch ta ce gwamnoni sun nuna babu kanshin gaskiya a kalaman Godswill Akpabio da ya ce sun samu karin kudi saboda halin yunwa.

Kara karanta wannan

Wasu ba su tsallake ba da aka tantance mutum 17 da Tinubu ya ba mukami a majalisa

Godswill Akpabio
A Majalisa Godswill Akpabio ya ce an rabawa gwamnonin jihohi N30bn Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Godswill Akpabio ya ce an turawa jihohi N30bn

Legit ta rahoto shugaban majalisar dattawan yana cewa an rabawa kowane gwamna N30bn bayan abin da aka saba ba shi a kowane wata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai girma gwamnan Oyo, Seyi Makinde, wanda shi ne mataimakin shugaba NGF ya fara karyata shugaban majalisar dattawan Najeriya.

Gwamnoni sun karbi N30bn daga FIRS?

Jami’an gwamnatocin jihohin Legas, Zamfara, Benuwai, Osun, Katsina da Enugu duk sun shaidawa jaridar ba a raba masu wani kudi ba.

Kwamishinan yada labarai na Legas, Gbenga Omotoso ya musanya wannan ikirari, yake cewa ba a aikowa gwamnatinsu N30bn ba.

"Ba gaskiya ba ne. Gwamnatin Mai girma Babajide Sanwo-Olu da Dr. Obafemi Hamzat ba ta samu wata N30bn daga hannun kowa ba.
Komai da kishin al’umma muke yi. Duk wani mai wannan ikirari ya fito da hujjoji. Gwamnanmu bai samu N30bn daga ko ina ba."

Kara karanta wannan

Yunwa: An ‘rabawa’ gwamnoni karin Naira Biliyan 30 kwanan nan, Shugaban Majalisa

- Gbenga Omotoso

Babu N30bn da aka aikawa jihar Osun

Kolapo Alimi wanda shi ne kwamishinan yada labarai da wayar da al’umma na jihar Osun ya yi irin wannan magana wajen wani taro.

Mista Kolapo Alimi ya ce kowa zai iya zuwa ya bincika, ba a aikowa jihar N30bn ba.

Katsina, Benuwai ba su karbi kudi ba

Maiwada Dammallam ya ce bai da labarin aikowa Katsina kudi na maganin yunwa, a matsayinsa na Darekta Janar na yada labarai.

A matsayinsa na kwamishinan kudi da tsare-tsaren kasafi a Benuwai, Michael Oglegba, ya yi mamakin jin kalaman Akpabio.

Da aka je taron FAAC a Abuja, Michael Oglegba ya tabbatar da babu gaskiya a zancen shugaban majalisar wanda ya taba yin gwamna.

Gwamnatin Tinubu ta ce babu lashe amai

Dala tana neman tabo N2, 000 a kasuwar canji, ana zargin litar man fetur ya kai N1000 a wasu wurare kamar yadda aka ji labari.

Kara karanta wannan

Buhari yayi maganar badakalar Mambilla da EFCC ta fara binciken manyan Gwamnati

Kaya sun kara tsada sannan rayuwa ta tsananta bayan cire tallafin fetur, amma Bola Tinubu ya ce gyara ake yi, kuma ba za a fasa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng