Yunwa: Gwamnan PDP Ya Fito Ya Fadi Gaskiya Kan Batun Ba Gwamnoni N30bn

Yunwa: Gwamnan PDP Ya Fito Ya Fadi Gaskiya Kan Batun Ba Gwamnoni N30bn

  • Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya mayar da martani kan iƙirarin cewa gwamnonin jihohi sun karɓi ƙarin Naira biliyan 30 daga gwamnatin tarayya
  • Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ne ya yi wannan zargin, inda ya ce rabon kuɗin daban yake da wanda aka saba ba su duk wata
  • Gwamna Makinde, ya ce babu wani abu makamancin haka, inda ya ce hukumar FIRS da Akpabio ya ce ta bayar da kuɗin ba ta da hurumin yin hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Iseyin, jihar Oyo - Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya ƙaryata iƙirarin da ke nuna cewa an ba ɗaukacin gwamnonin jihohi 36 Naira biliyan 30 kowannensu domin tunkarar ƙalubalen da ke addabar jihohinsu.

Kara karanta wannan

Labari mai daɗi: Farashin dala zai faɗi warwas a Najeriya nan ba da daɗewa ba, gwamna ya magantu

Musanta hakan da Makinde ya yi dai na zuwa ne a matsayin martani ga zargin shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

Makinde ya yi martani ga Akpabio
Gwamna Makinde ya musanta batun cewa FG ta ba gwamnoni karin N30bn Hoto: Godswill Obot Akpabio/Seyi Makinde
Asali: Facebook

Akpabio ya buga misali da wani rahoto da ba a tantance ba, wanda ke zargin gwamnatin tarayya ta ba gwamnoni ƙarin kuɗaɗe har N30bn.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

FIRS ba ta raba wa jihohi kuɗi - Makinde

A yayin ƙaddamar da babban masallacin Iseyin dake garin Iseyin, gwamnan ya nuna rashin jin daɗinsa kan kalaman Sanata Akpabio waɗanda baya tabbaci a kansu.

Kamar yadda TVC ta ruwaito, ya nuna shakku kan sahihancin iƙirarin Akpabio, inda ya nuna cewa hukumar tara haraji ta ƙasa (FIRS) ba ta da hurumin bayar da kuɗaɗe ga jihohi.

Ya kuma jaddada cewa kuɗaɗen da ke cikin asusun tarayya an ware su ne domin jin dadin ɗaukacin ƴan Najeriya, ba wai don raba wa wasu zaɓaɓɓun jihohi ba.

Kara karanta wannan

"Ina ji a jika": Tsohon gwamna ya koka kan daurin da EFCC ta yi masa

Gwamnan ya jaddada muhimmancin samar da amana ga jama’a a wannan lokaci mai muhimmanci, inda ya buƙaci shugabanni da su guji yin kalaman da za su tada zaune tsaye a siyasance.

Akpabio Ya Fadi Masu Ɗaukar Nauyin Zanga-Zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana masu ɗaukar nauyin zanga-zangar da ake yi kan tsadar rayuwa a ƙasar nan.

Shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa wasu ƴan tsiraru ne ke kitsawa tare da ɗaukar nauyin zanga-zangar da ake yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel