Ana Cikin Jimami Yayin da a Yau Za a Binne Tsohon Gwamnan APC a Kauyensu, Bayanai Sun Fito

Ana Cikin Jimami Yayin da a Yau Za a Binne Tsohon Gwamnan APC a Kauyensu, Bayanai Sun Fito

  • Marigayi tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu a yau Juma’a 23 ga watan Faburairu za a karkare bikin binne shi
  • Rahotannin da muke samu sun tabbatar za a yi bikin ne a cocin St. Andrew Anglican a kauyen Imola da ke Owo a cikin jihar
  • Idan ba a manta ba, marigayin ya rasu ne a ranar 27 ga watan Disambar 2023 a kasar Jamus bayan fama da jinya mai tsawo

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo – A yau Juma’a ce 23 ga watan Faburairu za a binne tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu.

Za a yi bikin binne Rotimi ne a cocin St. Andrew Anglican a kauyen Imola da ke Owo a cikin jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Tinubu yana bakin kokarinsa, ana yunwa a sauran kasashen waje Inji Sanatan APC

Za a karkare bikin zaman makokin gwamnan APC a yau Juma'a
Akeredolu ya mutu ne a watan Disambar 2023 a kasar Jamus bayan fama da jinya. Hoto: Rotimi Akeredolu.
Asali: Twitter

Yaushe marigayin ya rasu?

Marigayin ya rasu ne a ranar 27 ga watan Disambar 2023 a kasar Jamus bayan fama da jinya inda mataimakinsa ya dare karagar mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An fara bikin jimamin rasuwar gwamnan ne a birnin Ibadan da ke jihar Oyo inda a nan ne ya rayu a matsayin lauya kafin shiga harkokin siyasa.

An dauke gawarsa a ranar Laraba 21 ga watan Fabrurairu zuwa Owo da ke jihar Ondo inda nan ne mahaifarsa, cewar The Nation.

Manyan mutane da ‘yan siyasa da dama sun samu halartar bikin zaman makokin inda suka yi addu’ar samun rahama a gare shi.

Dan tsohon gwamnan, Babajide ya godewa jama’a da suka nuna musu kauna a wannan yanayin kunci da suke ciki.

Manyan bakin da suka halarci bikin

Ya ce yawan mutane da suka halarci bikin ya nuna tsantsar kauna da jama’a suka nunawa iyalansu gaba daya.

Kara karanta wannan

Farashin litar fetur ya kai N1,000 a wajen 'yan bumburutu yayin da aka fara dogon layi a gidajen mai

A cewarsa:

“Ina son in yi godiya ga jama’a kan wannan goyon baya da suka nuna mana musamman mutane Owo wanda ke nuna tsantsar kauna a gare mu.”

Yayin taron akwai Gwamna Lucky Aiyedatiwa wanda ya gaji kujerar marigayin da mataimakinsa, Olayide Adelami.

Sauran sun hada da mataimakin gwamnan jihar Kogi, Salifu Joel da Ministan matasa, Olawande Ayodele da sauransu, cewar BBC.

Lucky ya ayyana hutun kwana 2

Kun ji cewa, Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya ayyana hutun kwanaki biyu don karrama marigayi Gwamna Rotimi Akeredolu.

Ebenezer Adeniyan, babban sakataren yada labarai na gwamnan shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.