Yanzu Nan: Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban AMCON da Aka Yi Waje da Ahmed Kuru
- AMCON tayi sabon shugaba kuma dabban darekta bayan nade-naden da Bola Ahmed Tinubu ya sanar a hukumar tarayyar
- Gbenga Alade ake sa ran zai zama sabon shugaban AMCON da zarar Sanatoci sun tantance shi a majalisar dattawan Najeriya
- Shugaban kasa ya katse wa’adin Malam Ahmed Kuru wanda ya kamata ya bar hukumar AMCON a karshen shekara mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi nadin sababbin shugabannin da za su kula da hukumar AMCON a Najeriya.
Sanarwa ta fito a ranar Alhamsi cewa shugaban kasa ya nada Gbenga Alade a matsayin sabon Babban Darekta kuma shugaba.
Bola Tinubu ya fitar da nadin mukamai a AMCON
NTA ta ce Mai girma Bola Tinubu ya sanar da haka a wani jawabi da ya fito daga bakin mai magana da yawunsa, Ajuri Ngalale.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cif Ajuri Ngalale ya bayyana cewa an nada manyan Darektoci wadanda za su taya Alade aiki da zarar an iya tantance su a majalisa.
AMCON: Sai an tantance su a Majalisar dattawa
A dokar kasa da tsarin mulki, Sanatoci su kan tabbatar da wasu nade-naden mukamai da shugaban kasa zai yi kafin su shiga ofis.
Wadanda aka zaba a matsayin Darektoci a hukumar ta AMCON sun hada da Aminu Ismail, Adeshola Lamidi da kuma Lucky Adaghe.
Jawabin Shugaba Bola Tinubu
Mai taimakawa shugaban Najeriyan wajen yada labarai da hulda da jama’a ya bukaci wadanda aka zaba suyi aiki da kyau a hukumar.
"Shugaban kasa yana tsammanin maida hankali, nuna kwarewa da jajircewa daga sababbin wadanda aka ba mukamai"
"domin a tabbatar da ayyukan AMCON ya fi kyau, gaskiya sannan ya zo daidai da yunkurinsa na tsabtace harkokin kudin kasa"
"sannan a inganta kwarin gwiwa ga masu zuba hannun jari a tattalin arzikin Najeriya."
- Ajuri Ngalale
Da nadin Alade, an kawo karshen Ahmed Kuru wanda Muhammadu Buhari ya nada a 2015, kuma ya sabunta wa’adinsa a 2020.
An nada kwamishinoni a NPC
Ana da labari Isa Buratai, Abubakar Damburam da Sa’adatu Garba Dogon Bauchi sun samu mukaman kwamishinoni a hukumar NPC.
An tantance Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa amma majalisa ba ta amince da nadin Olakunle Sobukola da Oluseye Oluwatuyi tukuna ba.
Asali: Legit.ng