Wasu ba Su Tsallake ba da Aka Tantance Mutum 17 da Tinubu Ya Ba Mukami a Majalisa

Wasu ba Su Tsallake ba da Aka Tantance Mutum 17 da Tinubu Ya Ba Mukami a Majalisa

  • Sanatoci sun tabbatar da nadin kwamishinoni a NPC bayan kwamitin da ke kula da hukumar ya kammala aikinsa a majalisa
  • Majalisar dattawa ta amince mutane 17 daga cikin 19 da aka gabatar su shiga ofis kamar yadda Bola Ahmed Tinubu ya bukata
  • Jihohin Ondo da Ogun za su zama ba su da wakilci a hukumar NPC domin wadanda aka zaba ba su je gaban kwamitin ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin mutane 17 a matsayin kwamishinonin hukumar NPC mai alhakin shirya kidaya ta kasa.

A zaman da majalisar dattawa tayi na ranar Laraba, The Cable ta ce Sanatoci sun tantance sunayen wasu wadanda aka gabatar masu.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisar dattawa ya tona asirin masu ɗaukar nauyin zanga-zanga kan tsadar rayuwa a jihohi 4

Bola Tinubu
Bola Tinubu ya aika mukamai zuwa majalisa Hoto: @NgrSenate
Asali: Twitter

Daga cikin wadanda Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya aiko sunayensu tun Disamba, an yi nasarar amincewa da mutane 17 a jiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun ce an kai sunayen mutane 19 ne zuwa majalisar, a maimakon 20 da Cif Ajuri Ngalale ya sanar da farko a shafinsa.

NPC: Majalisar dattawa ta karbi mutane 17

A karshe mutane 17 sun samu amincewar majalisa, za su kama aiki gadan-gadan a NPC. Babu wakilai daga jihohin Ogun da Ondo.

Daga cikin wadanda aka amince da nadin na su akwai wadanda suke kan kujerar tun tuni, sannan akwai wanda yanzu suka zo.

Yadda aka amince da nadin kwamishinonin NPC

Shugaban kwamitin NPC a majalisar dattawa, Abdul Ningi ya gabatar da rahoton aikin da suka yi a gaban sauran takwarorinsa.

Sanatan na Bauchi ta tsakiya ya ce wadanda suka bayyana a gaban kwamitinsa sun cika sharudan da ake bukata wajen yin aikin.

Kara karanta wannan

Sanatoci sun lalubo yadda Gwamnatin Buhari ta haddasa asarar Naira tiriliyan 17

A karshe sauran sanatocin suka amince da wannan nadi bayan an yi zabe a zauren.

Su wanene aka nada a hukumar NPC?

Wadana aka tantance su ne: Emmanuel Eke (Abia); Clifford Zirra (Adamawa); Chidi Ezeoke (Anambra); sai Isa Audu Buratai (Borno).

Akwai Alex Ukam (Kuros Ribas); Blessyn Brume-Maguha (Delta), Jeremiah Ogbonna Nwankwegu (Ebonyi) da wani Tony Alyejina (Edo).

Sannan Ejike Ezeh (Enugu); Abubakar Damburam (Gombe); Uba Nnabue (Imo); Sa’adatu Garba (Kaduna) da Aminu Tsanyawa (Kano)

Majalisar dattawan ta kuma tantance Yori Afolabi (Kogi); Mary Afan (Plateau); Saany Sale (Taraba), a karshe akwai Ogiri Henry (Ribas).

Sauran biyun da ba a tantance ba su ne: Hon. Olakunle Sobukola da Oluseye Oluwatuyi.

Wasikar Bola Tinubu a kan nadi a NPC

A karshen shekarar bara, shugaban kasar ya zabi mutane 19 da za su rike kujerar kwamishinoni a hukumar NPC ta tarayya.

Ana da labari Mai girma Bola Ahmd Tinubu ya aiko takarda zuwa ga majalisar dattawan, ya nemi a tabbatar da nadin da ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel