Buhari ya sake nada Ahmed Kuru a matsayin MD na AMCON, Aminu a matsayin Darekta
- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi wasu muhimman nade-nade a hukumomin NDIC da AMCON
- Sanar da sabbin nade-nade na kunshe a cikin sanarwar da kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar ranar Litinin
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sake zaben Ahmed Kuru a matsayin manajan darekta a hukumar kula da kadarori ta kasa (AMCON).
Kazalika, ya amince da nada Eberechukwu Uneze da Aminu Isma'il a matsayin darektoci ma su cikakken iko na zangon wa'adin shekaru biyar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar a ranar Litinin.
DUBA WANNAN: A villa ake iskanci na gaske kuma Buhari ne jagora; Aisha ta mayar da martani a kan gargadin shugaba Buhari
A cewar Garba Shehu, shugaba Buhari ya aika sunayen mutanen zuwa majalisar dattijai domin neman amincewarta.
Kazalika, shugaba Buhari, a cikin wata wasikar daban, ya nemi majalisar dattijai ta amince da nadin Mista Bello Hassan a matsayin manajan darekta a hukumar NDIC.
DUBA WANNAN: Kungiyar Malaman Kano ta magantu a kan batun goyawa takarar Tinubu baya a 2023
A cikin wasikar, Buhari ya nemi majalisar ta amince da nadin Mustapha Muhammad Ibrahim a matsayin darektan mai cikakken iko a hukumar.
Legit.ng Hausa ta rawaito cewa gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce duk da kisan da mayakan kungiyar Boko Haram ke yi a Jihar, tsaro ya karu a jihar a karkashin mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Farfesa Zulum, ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayin da ya karbi bakuncin kungiyar dattijan arewa a karkashin jagorancin shugabanta, Ambasada Shehu Malami, da kuma sakatarenta, Audu Ogbeh.
Hakan na kunshe ne a cikin jawabin da gwamnatin jihar Borno ta fitar ranar Litinin mai taken 'Zulum: Duk da kashe-kashe, shaidu a kasa sun nuna cewa an fi samun zaman lafiya a karkashin mulkin Buhari a Borno.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng