Ma’aikata Sun Dakatar Da Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani da Suka Shiga a Jihar Arewa, An Fadi Dalili
- Kungiyar kwadago reshen Neja ta umurci daukaci ma'aikata a jihar da su koma bakin aiki a ranar Alhamis
- Wannan ya biyo bayan janye yajin aikin sai baba ta gani da kungiyar ta shiga a ranar Laraba, 21 ga watan Fabrairu a jihar
- An dauki matakin dakatar da yajin aikin ne yayin da ake ci gaba da tattaunawa tsakanin 'yan kwadago da bangaren gwamnati karkashin Mohammed Umar Bago
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Jihar Neja - Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) reshen jihar Neja, ta dakatar da yajin aikin sai baba ta gani da ta tsunduma a ranar Laraba, 21 ga watan Fabrairu.
An sanar da dakatar da yajin aikin ne bayan wani taron gaggawa da aka yi tsakanin shugabannin kungiyoyin NLC da TUC a garin Minna, babban birnin jihar a a daren Laraba, jaridar The Nation ta rahoto.
An yi zaman ne bayan wata ganawa da Gwamna Mohammed Umar Bago, da 'yan majalisarsa inda aka cimma matsaya kuma gwamnati ta yi tayin magance bukatun kungiyar kwadagon.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyoyin NLC da TUC sun yanke shawarar cewa ci gaban da aka samu ya isa a dakatar da yajin aikin yayin da ake ci gaba da tattaunawa.
Shugaban kungiyar ta RATTAWU, Kwamared Isah Mahmoud ne ya gabatar da kudirin dakatar da yajin aikin inda shugaban NAAT, IBBUL, Dr Hamzat Aliyu ya goyi bayan haka.
Jaridar The Nation ta kuma ruwaito cewa an bukaci daukacin ma'aikata da su gaggauta komawa bakin aiki nan take.
Wasu matsaya aka cimma a taron?
Yarjejeniyar da gwamnatin jihar Neja da kungiyar kwadago suka cimma shine cewa gwamnati za ta biya ma’aikata na jihar da kananan hukumomi N20,000 kowannensu a watan Maris.
Za a kafa kwamitin da zai kunshi wakilan majalisar dokokin Neja, da na zartaswa da 'yan kwadago don duba dokokin da ba gwamnati shawarwari.
Yarjejeniyar ta kuma bayyana cewa za a mayar da kaso 10 cikin 100 na fansho ga ma’aikatan da aka cire a kananan hukumomi, yayin da za a biya kudaden da suka rage na naira miliyan 218.7 a rukuni uku.
Legit Hausa ta zanta da wani ma'aikacin gwamnati mai suna Malam Abubakar don jin ta bakinta game da janye yajin aikin da kungiyar NLC ta yi.
Malam Abubakar ya ce:
"Ni ban ga amfanin tafiya yajin aikin ba ma tun farko. Kamata ya yi kungiyar ta san abin da take so sannan ta zamo mai tsayawa tsayin daka kan abubuwan da ta sanya gaba tun ma kafin ta kira yajin aiki.
"Mu dai mun wayi gari an ce kada mu je aiki da sunan yajin aikin sai baba ta gani, kwatsam a ranar da aka fara wannan mataki sai kuma aka ce mu koma bakin aiki an sasanta.
"Babu wata gamsasshiyar bayani da aka yi masa. Amma dai duk wanda ke jihar Neja ya san ma'aikata babu wani kyautatawa da ake yi mana.
"Muna dai fatan kamar yadda muka ji a kafafen yada labarai ace an samu maslaha mai dorewa ba wai a wayi gari gobe a kara zuwa mana da wani batun sabanin wannan ba."
Kungiyar NLC ta fara yajin aiki a Neja
A baya Legit Hausa ta rahoto cewa kungiyar NLC ta shiga aikin sai baba ta gani a jihar Neja wanda zai fara aiki daga ranar Laraba, 21 ga Fabrairu.
Kungiyar kwadagon ta ce ba za ta janye daga yajin aikin ba har sai gwamnati ta magance matsalolinsu.
Asali: Legit.ng