Jihar Benue ta saki shanu 210 ga makiyaya bayan karbar tarar Naira miliyan 5

Jihar Benue ta saki shanu 210 ga makiyaya bayan karbar tarar Naira miliyan 5

- Gwamnatin jihar Benue ta saki shanu 210 ga masu su biyo bayan biyan tarar Naira miliyan 5

- Jihar ta bayyana cewa, ba za ta iya janye dokar hana kiwo ba, dan haka dole makiyaya su kula

- Sakataren kungiyar Miyetti Allah ya roki da a sassautawa makiyayan kan duba dokar kiwon

Gwamnatin jihar Benue ta saki shanu 210 da masu gadin dabbobi a jihar suka kwace a Mbala dake fadar jihar a Makurdi, da Gbajimba a karamar hukumar Guma duk a jihar, Channels Tv ta ruwaito.

An mayar da shanun ga masu su bayan an biya tarar daban-daban na kimanin Naira miliyan 5.

Kwamandan masu kula da kiwo na jihar Benue, Linus Zaki, yayin da yake mayar da shanun ga masu su, ya gargade su da su guji karya dokar hana kiwo a fili ta shekarar 2017 tare da neman amincewa don kafa wuraren kiwo.

Ya gargadi makiyaya da kada su saba dokar hana kiwo a jihar, yana mai cewa jihar ba za ta dauki masu karya doka da wasa ba.

KU KARANTA: COVID-19: A fara yiwa jami'an gwamnati rigakafin kafin talakawa, in ji Tomori

Jihar Benue ta saki shanu 210 ga makiyaya bayan karbar tarar Naira miliyan 5
Jihar Benue ta saki shanu 210 ga makiyaya bayan karbar tarar Naira miliyan 5 Hoto: Channels Tv
Asali: UGC

"Mun kame shanu 140 a Mbala a ranar 11 ga Fabrairu, 2021, da shanu 70 a Gbajimba a ranar 16 ga Fabrairu, 2021. Gaba daya, muna mika shanu 210 ga masu su a yau.

"Ba za mu iya dakatar da aiwatar da dokar ba saboda haka dole ne makiyaya su koyi bin hanyar da ta dace," in ji Zaki.

Sakin shanun ya biyo bayan biyan Naira dubu 2 ga kowacce saniya na shanu 210; tare da 140 daga dabbobin da aka garkame na tsawon kwanaki 14 yayin da 70 daga cikinsu aka garkamesu na kwanaki takwas, wanda ya kai sama da Naira miliyan 5 kudaden da suka shiga asusun jihar.

Da yake magana a madadin masu shanun, sakataren kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah Ibrahim Galma ya roki a yi musu sassauci yana mai cewa tsarin kafa wuraren kiwo ya yi matukar fasaha da kimiyya ga Fulani makiyaya gama-gari.

Ya nuna damuwa kan yadda za a jure idan ba a samarwa jama'arsa wuraren kiwon da ake tunanin farawa.

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da dandalin rajistar rigakafin Korona ta yanar gizo

A wani labarin, Yajin aikin da dillalan kayan abinci suka shiga na kungiyar Hadin kan Dillalan Kayan Abinci da Shanu (AUFCDN), ya janyo hau-hawan farashin kayayyaki a yankin kudancin Najeriya, a cewar rahoton Daily Trust.

Kungiyar ta AUFCDN wacce bangare ne na kungiyar kwadago ta kasa wato (NLC), ta shiga yajin aikin ne a ranar Alhamis biyo bayan karewar wa'adin da ta bai wa Gwamnatin Tarayya na kwana bakwai da ta biya mata bukatunta.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.