An nemi manoma 3,383 an rasa bayan sun karbi bashin CBN N364m

An nemi manoma 3,383 an rasa bayan sun karbi bashin CBN N364m

- Akalla manoma 3,383 a jihar Taraba sun yi batan dabo da kudin bashi N364m da suka karba daga bankin CBN

-Mukaddashin shugaban kungiyar manoman shinkafan Najeriya, shiya jihar Taraba, Tanko Andami ya bayyana hakan

- Manoman sun karbi bashin ne tsakanin 2018 da 2019 don noma damin da rani

Kimanin manoma 3,383 da suka karbi bashin N364 million domin noman rani da damina tsakanin 2018 da 2019 a jihar Taraba sun yi batan dabo.

A rahoton The Guardian, reshen kungiyar manoman shinkafa a Najeriya na jihar Taraba (RIFAN), ta bayyana hakan.

Mukaddashin shugaban kungiyar, Tanko Andami, yace kudin da manoman kungiyarsa suka karba bashi sun ki biya, kuma da dama cikinsu sun gudu.

Andami ya bayyana mamakin dalilin da zai sa manoma su ki cika alkawuran da suka dauka ba.

Yace: "Babu ko daya cikinsu yanzu haka da ya dawo da kudin bashin da aka bashi, kuma da dama cikinsu sun gudu."

Babbar bankin Najeriya CBN ta basu bashin ne domin inganta noman shinkafa cikin manufar gwamnatin tarayya na ciyar da kasa shinkafa ba tare an shigo da su daga kasar waje ba.

An baiwa manoma daga kananan hukumomin Lau, Gassol, Wukari, Karim-Lamido, Ardo-Kila da Jalingo karkashin kungiyoyin hadin kai 185.

A cewar mataimakin shugaban kungiyar, Daniel Gani, ya ce yawancin manoman sun yi tunanin kyauta gwamnatin Buhari ta basu.

Ya kara da cewa wasu daga cikin manoman sun canza lambobin wayoyinsu da adireshin da suka bada, har yanzu ba'a samu nasarar samunsu ba.

Ya ce duk da cewa kungiyar na farfadowa ne yanzu, za ta iyakan kokarinta wajen ganin an kwato kudin bashin daga hannunsu.

An nemi manoma 3,383 an rasa bayan sun karbi bashin CBN N364m
An nemi manoma 3,383 an rasa bayan sun karbi bashin CBN N364m
Asali: UGC

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng