Mutane Sun Tare Motar Dangote, An Wawushe Abinci da Yunwa Ta Bugi Yaro da Babba

Mutane Sun Tare Motar Dangote, An Wawushe Abinci da Yunwa Ta Bugi Yaro da Babba

  • Ana tunanin mutane sun jawo kamfanin Dangote Group asara mai yawa yayin da aka kai wa motarsa hari a Katsina
  • Bidiyon da yake yawo a shafukan sada zumunta ya nuna dinbin mutane sun shiga wasoson abinci daga motar Dangote
  • Zuwa yanzu ana kara kukan yunwa da talauci, cin abinci ya gagari mafi yawan marasa karfi a jihohin kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Katsina - Ana zargin cewa mutane sun tare motar kamfanin Dangote Group, sun yi gaba da kayan abincin da aka kinkimo.

Rahoton Aminiya ya ce ana zargin wannan mummunan lamari ya auku ne a jihar Katsina da ke yankin Arewacin Najeriya.

Dangote
Motar Dangote Hoto: Getty Images (Hoton nan bai da alaka da labarin)
Asali: Getty Images

Bidiyon 'wawar' Dangote

Wani bidiyo ya nuna yadda mutane su ke wawar kayan abincin da kamfanin Dangote wanda ya yi fice a Afrika ya dauko.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Kano da sauran jihohi 3 da aka gudanar da mummunar zanga-zanga a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Faifen bidiyon yana ta yawo a kafofin sada zumunta na X wanda aka fi sani da Twitter da kuma WhatsApp a ranar Talata.

Za a iya ganin maza, mata da yara duk suna wasoson abinci daga motar a lokacin da jama’a su ke kukan yuwa a fadin Najeriya.

Ana zargin tsare-tsaren gwamnatin Bola Tinubu sun jawo karin talauci da tsadar rayuwa.

Za a kai abinci kasar Nijar?

Majiyar ta ce motar tana hanyar zuwa Jamhuriyyar Nijar ne domin kai kayan abinci a lokacin da ake murnar farashi ya yi sauki.

Jaridar ta ce kamfanin ya tabbatar da an kai wa motarsa hari, amma ya musanya batun cewa kasar Nijar za a wuce da abincin.

A yanzu mahukanta sun dage wajen hana a fita da abinci daga Najeriya zuwa kasashen ketare saboda irin halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

An maida motocin abinci 50 Najeriya, za su shiga kasar Nijar bayan umarnin Tinubu

Bayan haka, a shekarar bara kuma gwamnatin Najeriya ta rufe iyakarta da makwabciyar saboda sojoji sun yi juyin mulki.

A wata sanarwar kuma kamfanin ya karyata rahoton da yake cewa an kama motarsa za ta fita da siminti zuwa kasar Kamaru.

Yunwa: Yaran Tinubu sun bada hakuri

Ana da labari yaron shugaban kasa, Seyi Tinubu ya ce dole al’umma ta jure kuncin rayuwar da aka burma idan ana so gobe tayi dadi.

Yaran shugaban Najeriya sun ce a kara hakuri kadan, komai zai dawo daidai a mulkin Bola Tinubu duk da matsin da aka shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng