An Maida Motocin Abinci 50 Najeriya, Za Su Shiga Kasar Nijar Bayan Umarnin Tinubu

An Maida Motocin Abinci 50 Najeriya, Za Su Shiga Kasar Nijar Bayan Umarnin Tinubu

  • Wasu motoci kimanin 50 da aka cika da kayan abinci daga Najeriya sun gagara shiga Nijar kamar yadda aka yi niyya
  • Hukumar ZARTO ta tsare wadannan manyan motoci a garin Zurmi, ta umarci su koma a saida kayayyakin a Najeriya
  • Ana hana ‘yan kasuwa fita da buhunan abinci a sakamakon umarnin da shugaban kasa ya bada a makon da ya gabata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Zamfara - Manyan motoci da ke dauke da kayan abinci da nufin za a kai kasar Nijar sun fada hannun hukuma a jihar Zamfara.

A ranar Litinin, Punch ta ce hukumar kula da sufuri ta jihar Zamfara ta tsare wasu motocin abinci 50 a kan hanyar zuwa Nijar.

Abinci
Mota da abinci (Hoton bai da alaka da labari) Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

An hana fita da abinci zuwa Nijar

Kara karanta wannan

Farfesa ya bayyana kuskuren da Tinubu ya fara tafkawa kafin shiga Aso Villa

An tsare wadannan motoci ne bayan umarnin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bada da ya haramta a boye kayan abinci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganin yadda farashin abinci ya tashi, Mai girma Bola Tinubu ya shirya yaki da masu koye kaya, an fara rufe shagunan ‘yan kasuwa.

ZARTO ta tare motocin abinci

Mai magana da yawun bakin hukumar ZARTO, Sale Shinkafa ya ce an yi yunkurin haurawa da motocin abincin ne zuwa jamhuriyyar Nijar.

Nan take jami’an ZARTO suka tare motocin, aka maida su Najeriya domin a saida a can. Ana tunanin hakan zai karya farashi a kasuwa.

A jawabin da Sale Shinkafa ya yi, an fahimci hukuma ba ta tsare motocin ko ta tura jami’anta suyi mata rakiya ba, an daina kora su ne.

ZARTO sun hana a shiga da abincin zuwa Nijar saboda halin da ake ciki a Najeriya yayin da alaka ta kuma yi tsami tsakanin kasashen.

Kara karanta wannan

Jerin jihohin Najeriya 10 da aka fi samun kayan abinci da tsada, Kogi na kan gaba

Jami'ai sun tsare iyakar Najeriya da Nijar

Wani mazaunin garin Zurmi a jihar ta Zamfara ya shaidawa manema labarai ta wayar salula cewa an tare motocin ne a kauyen Jaja.

Kauyen Jaja yana kan iyaka tsakanin karamar hukumar Zurmi a Zamfara da kasar Nijar. 'Yan bindiga sun addabi yankin a shekarun nan.

Ana hana kai abinci kasashen waje

Rahoton ya ce ana zargin manyan ‘yan kasuwa suna sayen buhunan abinci su kai kasashen Afrika irinsu Nijar da Kamaru a boye.

Kafin nan, hukumar kwastam ta tare tireloli 15 da suka dauko kayan abinci daga Sokoto zuwa iyakar Najeriya da jamhuriyyar Nijar.

Yunwa za ta jawo zanga-zanga a sakatariyar APC

A rahoton da muka fitar da safen nan, an ji wahalar da ake ciki a yau ba ta bar ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai-ci da ‘yan adawar gwamnati ba.

Fetur ya kara kudi, kaya sun kara tsada, abinci ya tashi a kasuwanni bayan Bola Tinubu ya karbi mulki ya fito da tsare-tsare a mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng