Kotu ta yanke wa 'yan mata hukuncin ɗauri saboda bidiyon rawan baɗala a TikTok
Wata kotu a kasar Masar ta yanke wa wasu mata biyar hukuncin shekaru biyu a gidan gyaran hali saboda wallafa wani bidiyon rawan baɗala a dandalin sada zumunta ta TikTok.
Masu binciken sun ce matan biyu sun hada da daliba mai shekara 20, Haneen Hossam da Mawada Eladhm mai shekaru 22 sai kuma wasu mata uku da ke kula musu da shafukan sada zumuntan.
An kuma ci matan tarar fam din kasar masar 300,000 kowanensu saboda "cutar da al'adun iyali na kasar Masar da badala da koyar da safarar mutane," a cewar sanarwar da masu bincike suka fitar.
DUBA WANNAN: Na fi jin dadin yi wa mata da suka manyanta fyade - Mai laifi
Haneen Hossam da Mawada Eladhm sun yi suna saboda TikTok inda suka tara miliyoyin mabiya saboda bidiyoyin da suke wallafawa inda suke rawa, kwalliya, daukan hoto a motoci da barkwanci.
Sai dai sunan da suka yi a shafukan sada zumuntar ya zame musu matsala a kasar da mutum kan iya tsintar kansa a gidan gyaran hali a kan laifuka masu wahalar fahimta kamar "amfani da shafin sada zumunta ta hanyar da ba ta dace ba," "gurbata tarbiyya," ko"yada labaran bogi."
Lauyoyinsu sun sha alwashin daukaka kara game da hukuncin da aka yanke musu.
Lauyan Eladhm, Ahmed el-Bahkeri, ya tabbatar da hukuncin da aka yanke mata inda ya ce masu binciken suna ganin hotuna da bidiyon Eladhm a matsayin abin kunya da cin mutunci.
"Eladhm ta rika kuka a kotu tana jinjina hukuncin da aka yanke mata, Shekaru biyu? Fam din Masar 300,000? Wannan abu ne mai tayar da hankali," a cewa Samar Shabana, mataimakin lauyan ta.
"Su kawai mabiya suke so. Ba su da hannu cikin aikata karuwanci kuma ba su san cewa haka masu binciken ke kallon abubuwan da suke wallafawa ba," inji ta, yayin da ta ke magana a kan rubutun da suka wallafa na bawa mata shawarar su rika sayar da bidiyonsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng