Tsadar Rayuwa: Kungiyar ASUU Ta Rasa Farfesoshi 46 a Manyan Jami'o'in Arewa, Ta Tura Sako

Tsadar Rayuwa: Kungiyar ASUU Ta Rasa Farfesoshi 46 a Manyan Jami'o'in Arewa, Ta Tura Sako

  • Yayin da ake cikin mummunan hali a Najeriya, kungiyar ASUU ta ce ta rasa Farfesoshi 46 saboda tsadar rayuwa
  • Kungiyar reshen birnin Abuja ta ce hakan bai rasa nasaba da halin kunci da kuma rashin inganta aikin daga gwamnati
  • Kwadinetan kungiyar reshen Abuja, Salahu Muhammed shi ya bayyana haka ga manema labarai a yau Litinin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU) ta bayyana irin asarar da ta tafka saboda halin kunci da ake ciki.

Kungiyar ta ce akalla Farfesoshi 46 suka rasa ransu saboda halin kunci da rashin inganta ma'aikata., Cewar Punch.

Yawan Farfesoshi da ASUU ta rasa kan wani dalili 1 a Najeriya
ASUU ta fusata kan rashin Farfesoshi 46 da ta yi saboda tsadar rayuwa. Hoto: House of Reps.
Asali: Facebook

Mene dalilin rasa malaman da ASUU ta yi?

Kara karanta wannan

'Yar Najeriya ta saka kowa alfahari, ta zama mafi kwazo a makarantar kiwon lafiya ta Burtaniya

Ta ce har ila yau, rashin yanayi mai kyau na aikin ya yi sanadin mambobin nasu a Jami'o'in Abuja da Jami'ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna a jihar Neja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran Jami'o'in sun hada da Jami'ar jihar Nasarawa da ke Keffi sai kuma Jami'ar Ibrahim Babangida da ke Lapai a jihar Neja.

Kwadinetan kungiyar reshen Abuja, Salahu Muhammed shi ya bayyana haka ga manema labarai, cewar Eagles online.

Salahu ya ce a kwanakin nan kungiyar ta rasa Farfesa Johnson Oyero da ke Jami'ar Fasaha a Minna saboda rashin iya siyan magani.

Ta koka kan yarjejeniya da Gwamnati

A cewar kungiyar:

"A cikin shekaru 10, mambobinmu na barin kasar don neman ci gaba a rayuwarsu, wanda hakan ke kashe wa sauran gwiwa saboda rashin kula da su.
"Har ila yau, kungiyar ta rasa mambobinta da ke zangon Abuja kusan 46 saboda halin kunci rayuwa.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnonin PDP sun nemi Tinubu ya yi murabus, sun fadi dalili

"Sannan a 'yan kwanakin nan, mun rasa Farfesa Johnson Oyero a Jami'ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna kan rashin samun magani."

Har ila yau, kungiyar ta yi Allah wadai ganin yadda Gwamnatin Tarayya ta gaza mutunta yarjejeniyar da suka yi da ita, The Capital ta tattaro.

Majalisa ta tsaya wa 'yan Najeriya

Kun ji cewa Majalisar Dattawa ta ce ba za ta taba bari a kara kudin man fetur da wutar lantarki ba.

Majalisar ta ce su na Majalisar ce don 'yan Najeriya ba don kansu ba don haka dole su kare muradun al'umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel