Karfe 2 na dare, Zulum ya dira asibitin gwamnati na Monguno, zai kara 30% na albashi ga likitoci a LGs 7

Karfe 2 na dare, Zulum ya dira asibitin gwamnati na Monguno, zai kara 30% na albashi ga likitoci a LGs 7

  • Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kai ziyara babban asibitin Monguno da karfe 2 na daren Asabar
  • Zulum ya amince da karin albashi kashi 30 na likitocin kananan hukumomin Monguno, Ngala, Dikwa, Kukawa, Kala-Balge, Abadam da Banki
  • Gwamnan Bornon ya yi umarnin samar da karin gidajen ma'aikata a asibitin, samar da tuka-tuka da na'urar wuta mai amfani da hasken rana

Monguno, Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, yayin da ya kai ziyara babban asibitin a Konguno, ranar Asabar, ya sanar da amincewa da karin kashi 30 cikin dari na albashin likitoci a kananan hukumomi bakwai ba tare da tsammani ba.

Baya ga likitoci, ma'aikatan lafiya, anguwan zoma, masu gwaje-gwaje a dakin bincike, masu hada magunguna da sauran ma'aikatan lafiya na kananan hukumomi bakwai suma za su amfana da karin kashi 30 bisa dari na albashinsu, don karfafasu wajen gudanar da aiki mai nagarta da kula da fannin lafiya yadda ya dace.

Kara karanta wannan

Ba za'a daina kashe mutane ba muddin ba'a bari jama'a su mallaki nasu bindigogin ba, Dan majalisa

Karfe 2 na dare, Zulum ya dira asibitin gwamnati na Monguno, zai kara 30% na albashi ga likitoci a LGs 7
Karfe 2 na dare, Zulum ya dira asibitin gwamnati na Monguno, zai kara 30% na albashi ga likitoci a LGs 7. Hoto daga @GovBorno
Asali: Twitter

Kananan hukumomin: Monguno, Ngala, Dikwa, Kukawa, Kala-Balge Abadam da Banki cikin Bama wanda suke daga cikin wuraren da 'yan Boko Haram suka tarwatsa a shekarar 2014, ba tare da an zauna ba na kusan shekaru takwas har zuwa rufe sansanin 'yan gudun hijara da masu neman mafaka aka yi.

Bulaliyar majalisar dattawa, Barr. Muhammad Tahir Monguno ne ya raka Zulum babban asibitin misalin karfe 1:00 dare suna can har zuwa karfe 2:00 dare.

Dr. Solomon Tiza, shugaban jami'an kiwon lafiya ne ya tarbeshi, gami da kewayawa dashi asibitn.

Gwamnan ya yi umarni da gina karin gidajen ma'aikata, samar da tuka-tuka da wutar Sola don bunkasa ayyuka a asibitin.

Da farko dai, a watan Janairu, 2022, Zulum ya daga albashin duka likitocin Borno zuwa matakin da gwanatin tarayya ke biya, don kawo karshen matsalar yadda likitocin jihar ke komawa asibitocin gwamnati don samun albashi mai tsoka.

Kara karanta wannan

Sakin Dariye da Nyame: Bayan kwashe shekaru 11 a kotu, da kashe miliyoyin kudi, Shikenan: Lauyoyin EFCC

A shekaru ukun da gwamnan ya yi a mulki, ya amince da daukan ma'aikatan lafiya 676 wadanda suka hada da sama da likitoci 40 masu jinya 241, anguwannin zoma da sauransu.

Zulum ya kwana a Monguno, wanda ke arewacin jihar daga ranar Alhamis zuwa ranar Juma'a, don sauraran koken jama'a.

Gwamna ya je Monguno tare da Chief Muhammad Tahir Monguno, Kwamishinan gine-gine, da sake tsarin guri, Injiniya Mustapha Gubio, Kwamishinan Shari'a, Barista Kaka Shehu Lawan da tsohon kwamishinan noma da kiwo, injiniya Bukar Talba da dai sauransu.

Hotuna: Zulum ya gwangwaje 'yan gudun hijirar Monguno da N275m, kayan abinci, sutura

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya garzaya garin Monguno tun ranar Alhamis inda ya duba yadda ake raba miliyan dubu dari biyu da saba'in da biyar tare da buhunan abinci da kuma sutturu da aka raba wa gidaje 90,000 na 'yan gudun hijira.

Kara karanta wannan

Hotuna: Zulum ya gwangwaje 'yan gudun hijirar Monguno da N275m, kayan abinci, sutura

Wannan irin tallafin, wanda Zulum ya saba kai wa tun shekaru uku da suka gabata, yana daga cikin kokarinsa na karfafa guiwar yankunan da hare-haren Boko Haram suka shafa, taimaka musu da yanayin rayuwa yayin da suke komawa noma da sauran kasuwanci domin tallafawa rayuwarsu.

Tallafin kudin ana ganin amfaninsa domin kuwa yana hana jama'a zama masu leken asiri ga 'yan Boko Haram sakamakon tsananin talauci, da kuma kwadayin yadda suke bai wa jama'ar N5,000 a matsayin kyautatawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel