Gwamna Ya Kawo Shawara 1 Rak da Ta Rage Wajen Kawo Karshen ‘Yan Bindiga a Jihohi
- Mai girma Uba Sani ya ce za a yi ta fama da matsalolin tsaro da garkuwa da mutane a jihohi muddin ba a yi gyaran da ya kamata ba
- Gwamnan jihar Kaduna ya sake nanata maganar kafa ‘yan sanda a jihohin kasar nan, yana tunanin wannan ita ce mafitar da ta rage a yau
- A wuraren da gwamnonin nan suka tashi tsaye wajen kafa ‘yan banga na musamman, Gwamnan ya ce an fara samun saukin tsaro
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ce rashin tsaro da ya dabaibaye yankunan jihohin Arewacin kasar yana da magani.
Mai girma Uba Sani ya fitar da jawabi inda yake bayanin yadda wannan matsala ta addabi bangarori da yawa na Arewacin kasar nan.
Gwamnan na Kaduna ya yi wannan jawabi ne jim kadan da ‘yan bindiga su ka kai hari a kauyen Gindin Dutse Makyali a garin Kajuru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Uba Sani yana son 'yan sanda a jihohi
Tashar Channels ta rahoto gwamnan yana cewa sai an canza tsarin da ake kai a kasar, yana ganin akwai bukatar ‘yan sandan jihohi.
Uba Sani ya ce tsawon watanni shida da suka wuce, yana ta bada shawarar a kafa ‘yan sanda a matakan jihohi domin a samu tsaro.
A hirar da aka yi da shi, gwamna Uba Sani ya ce ya ji dadin yadda ya ga sauran abokan aikinsa suna kawo shawarar da yake a kai.
“Nayi farin ciki da makonni baya wasu gwamnoni suka taya ni fafutukar kafa ‘yan sandan jihohi kuma murya guda ce.”
“Wasu gwamnoni sun yi nisa a ‘yan watannin bayan nan ta hanyar kafa dakarun sa-kai na musamman a jihohinsu.”
- Gwamna Uba Sani
Gwamnan Kaduna ya ce sai an dage
Game da hare-haren da aka kai a yankin Kufena a karamar hukumar Kajuru, gwamnan ya shaidawa gidan talabijin halin da ake ciki.
Sai dai duk kokarin da dakaru za su yi a yanzu, tsohon Sanatan na tsakiyar Kaduna ya nuna ba zai yi dogon tasiri kamar yadda za a so ba.
“Ba za a iya ba kuma ba za a taba shawo kan rashin tsaro ba sai gaba daya mun yarda a kafa ‘yan sandan jihohi da gaggawa.
Idan ka na da ‘yan sa-kai ko ‘yan banga, wace doka ta hallata masu rike bindigar AK-47?”
- Gwamna Uba Sani
Matsalar Gwamnan CBN
A wani rahoton kuma an ji cewa awai mutane akalla uku da ake zargi sun taimaka aka sace kusan N3tr daga bankin CBN a shekarar 2023.
Gwamnatin Najeriya ta hada-kai da ‘yan sanda na Interpol domin a cafko; Adamu Abubakar, Imam Abubakar da Odoh Ochene a duniya.
Asali: Legit.ng