Wasan Karshe Na Afcon: Gaskiyar Batu Kan Bidiyon da Ke Zargin Golan Ivory Coast da Sanya Guraye
- Kashin da Super Eagles ta Najeriya ta sha a wasan karshe na AFCON na 2023 ya sa wasu na zargin ‘yan wasan Ivory Coast da amfani da tsafi
- Sai dai, binciken da aka yi ya nuna cewa, sam ba gaskiya bane, inda kafafen yada labarai da dama suka bayyana hujja kan haka
- Duk da haka, an ga wani bidiyon golan kwallon kafa da ba a san ko na wacce kungiya bace ganin sunansa da bayanansa basu bayyana ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Gasar cin kofin zakarun Afrika na AFCON ya kare a makon da ya gabata, inda kasar Ivory Coast ta yiwa Najeriya ci 2 da 1 a wasan karshe.
Sai dai, wasu da ke zuba ido a kafafen sada zumunta sun zargi cewa, akwai lauje cikin nadi a nasarar da kasar ta Ivory Coast ta samu.
A hujjar da wasu ma’abota Twitter ke kafawa, akwai yiwuwar golan Ivory Coast, Yahia Fofana ya yi amfani da tsafi a wasan, har ta kai ga rasawar Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin wadanda suka yada bidiyon da ke nuna alamar hakan har da tsohon sanata, Shehu Sani da fitaccen dan jairda Reuben Abati.
‘Yan Najeriya na zargin Ivory Coast da amfani da tsafi
A wani rubutun da ya yada a Twitter a ranar 14 ga watan Faburairu, Shehu Sani ya yi kira ga FIFA da ta gaggauta bincike tare da daukar mataki idan hakan ta tabbata.
Hakazalika, a babin zolaya, Shehu Sani ya ce idan ba a dauki mataki ‘yan Najeriya ma za su tattari guraye da layunsu a wasannin gaba.
"Ya kamata a yiwa 'yan Najeriya ka'ida wajen hawa shafukan sada zumunta", gwamnan Ekiti ya tono batu
A cewarsa:
“Ya kamata FIFA ta bincike zargin amfani da guraye da golan Ivory Coast ya yi kamar yadda hotuna ke nunawa tare da daukar mataki. Iadn FIFA ta gaza yin haka, a nan gaba, za mu tafi da tawagar bkayenmu.”
Reuban Abati kuwa cewa ya yi:
“Daga karshe dai bidiyon golan Ivory Coast da ake zargin ya sanya guraye a wasan AFCON ya jawo cec-kuce.”
Meye gaskiyar lamarin golan Ivory Coast da guraye?
Sai dai, wasu kafafen labarai sun binciko gaskiyar lamari, inda suka tabbatar da cewa, golan da aka gani ba na Ivory Coast bane, golan Senegal ne mai lambar riga 16 da da suna ASC JARAAF.
A bidiyon da Legit ta gani, mun gano cewa, dan wasan da aka gani sunansa Abdoulaye Diakhate da ke bugawa ASC Jaraaf, wata kungiyar kwallon kafan Senegal.
Ya sanya wani abu da ake ganin ya yi kama da guru a yayin da yake murna a daya daga wasannin da ya buga.
Wannan na nufin, tabbas bidiyon bai da alaka da wasan AFCON balle kuma wasan karshe da aka buga tsakanin Najeriya da Ivory Coast.
Martanin 'yan Najeriya bayan rasa kofin AFCON
A bangare guda, 'yan Najeriya da dama sun bayyana bacin ransu da abin da ya faru a wasan karshe na AFCON da aka gudanar.
Da yawa sun daura laifin hakan ga shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, inda suka bayyana ra'ayoyinsu a kafafen sada zumunta.
Ba wannan ne karon farko da Najeriya ke rasa damar daukar kofin AFCON ba, hakan ya sha faruwa.
Asali: Legit.ng