Tsadar Rayuwa: Sheikh Jingir Ya Tura Sakon Roko Ga Tinubu Kan Cire Tallafi, Ya Fadi Dalilansa
- Shugaban Majalisar Malaman kungiyar Izalar Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya roki Tinubu kan cire tallafin mai
- Sheikh Jingir ya roki Shugaba Tinubu ya dawo da tallafin mai don samun sauki ga al’ummar Najeriya da ke wani hali
- Jingir ya bayyana haka ne yayin wata nasiha a wajen wa’azin kasa da aka gunadar a birnin Tarayya Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Yayin da ake cikin mawuyacin hali a Najeriya, Sheikh Sani Yahaya Jimgir ya sake magana kan lamarin.
Shugaban na Izalah bangaren Jos ya bukaci Shugaba Tinubu ya dawo da tallafin mai don samun sauki ga al’umma.
Mene Jingir ke cewa ga Tinubu?
Jingir ya bayyana haka ne yayin wata nasiha a wajen wa’azin da aka gunadar a birnin Tarayya Abuja, cewar Aminiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kungiyar ya yi roko na musamman ga Tinubu da ya dawo da tallafin da ya cire don samun sassauci.
Wannan na zuwa ne yayin da ake cikin wani hali a kasar tun bayan cire tallafin da Tinubu ya yi a watan Mayun 2023.
Rokon Jingir ga Tinubu
A cewarsa:
“Shugaban kasa don girman Allah ka dawo da tallafin mai da ka cire, domin mu samu sassaucin matsin rayuwar da muke ciki.”
“Ana gaya mana cewa, an samu naira tiriliyan uku dalilin cire tallafin mai, a yayin da za a samu mutum daya a cikin barayin Najeriya da zai saci sama da wadannan kudade a lokaci guda.
“Ya kamata gwamnati ta kama masu sace kudaden kasar kuma ta dawo mana da tallafin man da ta cire.”
Wannan na zuwa ne bayan Sarkin Musulmi ya bukaci a yi gaggawar daukar mataki kafin komai ya dagule a kasar.
Jingir ya kalubalanci masu zarginsa
A baya, kun ji cewa, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi magana kan tikitin Musulmi da Musulmi a Najeriya.
Jingir ya ce bai taba dana sanin zabar tikitin ba inda ya ce duk wanda ke jiran ya yi dana sani ya na bata lokacinsa ne.
Wannan na zuwa ne yayin da ake cece-kuce kan zaban Tinubu da malamin ya bukaci a yi a baya.
Asali: Legit.ng