AFCON: Gwamnan PDP Ya Bai Wa Dan Wasan Super Eagles Kyautar N20m, Ya Gwangwaje Sauran Tawagar

AFCON: Gwamnan PDP Ya Bai Wa Dan Wasan Super Eagles Kyautar N20m, Ya Gwangwaje Sauran Tawagar

  • Tun bayan kammala gasar AFCON a kasar Ivory Coast, ‘yan wasan Super Eagles ke samun kyaututtuka daban-daban
  • Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya bai wa golan tawagar Super Eagles, Stanley Nwabali kyautar naira miliyan 20
  • Gwamnan har ila yau, ya bai wa sauran tawagar da suka halarci taron kyautar naira miliyan 30 don kara musu karfin gwiwa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ribas – Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya bai wa golan Najeriya, Stanley Nwabali kyautar miliyan 20.

Fubara ya yi wannan kyauta ce ga golan bayan bajintar da ya nuna a gasar AFCON da aka kammala a Ivory Coast.

Gwamnan PDP ya gwangwaje dan wasan SupEr Eagles da kyauta
Gwamna Fubara na Rivers ya bai golan Najeriya N20m da lambar yabo. Hoto: @SimFubaraKSC.
Asali: UGC

Wace kyauta Fubara ya bai wa dan wasan?

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun aikawa Bola Tinubu sako kan mugun hadarin da ake fuskanta

Gwamnan wanda ya karbi bakwancin Nwabali da sauran shugabannin Super Eagles ya bai wa Nwabali lambar girma a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Siminalayi ya karbi bakwancin ‘yan wasan ne a ranar Juma’a 16 ga watan Faburairu a Port Harcourt da ke jihar.

Har ila yau, gwamnan ya bai wa tawagar da suka samu halartar taron kyautar naira miliyan 30, cewar Channels TV.

Ya yabawa Nwabali wanda haifaffen jihar ce saboda irin rawar da ya taka a gasar da aka kammala.

Kyautar da sauran tawagar suka samu daga Fubara

Ya ce:

“Ina son taya dan uwanmu Stanley Nwabali murna tare da sauran al’ummar jihar Ribas da kuma tawagar gaba daya.”

Har ila yau, Fubara ya kuma yi alkawarin ci gaba da ayyukan alkairi don daklie matsalolin jihar gaba daya, cewar TV360.

Kara karanta wannan

A karshe, tsohon gwamnan Kaduna ya gaji da zama, ya sauya sheka zuwa APC, ya fadi dalili

Ya ce zai ba da kulawa wurin ganin ya samar da wani yanayi mai kyau ga ‘yan jihar don ci gaba a ko wane fanni.

Musa ya yi magana kan makomarsa

Kun ji cewa kyaftin din tawagar Super Eagles, Ahmed Musa ya yi magana kan makomarsa bayan kammala gasar AFCON.

Musa ya ce har yanzu shi dan kwallo ne kuma ya na shirye ya amsa gayyata a duk lokacin da aka bukace shi.

Ya kuma yi magana kan rashin buga wasa inda ya ce babban abu mai muhimmanci shi ne yin nasara ko da kuwa bai buga ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel