Jami'an 'Yan Sanda Sun Samu Gagarumar Nasara Kan 'Yan Bindiga a Jihar Arewa
- Rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da kashe wani ɗan bindiga a yayin wani artabu da jami'anta suka yi da miyagu
- Rundunar ta kuma ce ta cafke mutum 15 da ake zargin ƴan bindiga a samamen da ta kai lokuta daban-daban a jihar
- Kwamishinann ƴan sandan jihar wanda ya tabbatar da hakan, ya kuma bayyana cewa jami'an ƴan sandan sun ƙwato makamai da motoci daga hannun miyagun
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ta kashe wani da ake zargin ɗan bindiga ne tare da cafke wasu ragowar mutum 15.
Ƴan sandan sun samu wannan nasarar ne a samamen da suka kai lokuta daban-daban a jihar, cewar rahoton Channels tv.
Hukumomin ƴan sandan a jihar ta yankin Arewa-maso-Yamma sun ce sun kuma ƙwato muggan makamai a hannun ƴan bindigan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar ta bayyana cewa makaman da ta ƙwato sun haɗa da bindiga mai sarrafa kanta guda ɗaya, bindigogi ƙirar AK-47 guda uku da tarin alburusai daga hannun waɗanda ake zargin, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.
Yadda ƴan sanda suka kashe ɗan bindigan
Yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a hedikwatar rundunar a ranar Alhamis, kwamishinan ƴan sandan jihar Sokoto, Hayatu Kaigama, ya ce an kashe ɗan bindigan ne a wata arangama da wasu ƴan ta’adda a ƙaramar hukumar Gwadabawa ta jihar.
Kwamishinan ya kuma ce an kama wani da ake zargin ɗan ta’adda ne da ya ci gajiyar shirin afuwa na baya-bayan nan da aka yi a ɗaya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma, da wanda ake zargin ya ƙware wajen magance raunukan harsasai na ƴan ta’adda.
An samu nasarar kwato motocin ƴan ta’addan guda biyu yayin da ƴan sandan suka ce suna bin sahun ƴan bindigan da suka tsere domin ganin an gurfanar da su gaban kotu.
An Cafke Masu Garkuwa da Mutane a Sokoto
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ta ce ta cafke wasu mutum biyar da take zargin masu garkuwa da mutane ne da ke aiki a jihar.
Rundunar ƴan sandan ta ce ta cafke mutanen ne dauke da bindigogi uku kirar AK-47, harsasai guda 90 da kuma gidan harsasai na AK-47 guda uku.
Asali: Legit.ng