Yadda Wani Mutum Ya Hallaka Makwabcinsa Saboda Akuya, Ya Shiga Hannun 'Yan Sanda

Yadda Wani Mutum Ya Hallaka Makwabcinsa Saboda Akuya, Ya Shiga Hannun 'Yan Sanda

  • An zargi wani mutum mai suna Kolawole Akinsanya ya gayyato 'yan daba don su yi wa makwabcinsa, Lukmon Ajibola, duka har ya mutu a jihar Ogun
  • Akinsanya ya hada kai da 'yan daba bayan marigayin ya tunkare shi kan kashe masa akuya don ta ci masa doya
  • Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Ogun sun kama tare da tsare Akinsanya sannan suna neman sauran mutanen da suka tsere

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Rundunar 'yan sanda ta kama wani mutum mai suna Kolawole Akinsanya kan zargin hada kai da wasu bata gari don yi wa makwabcinsa, Lukmon Ajibola, dukan mutuwa.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa lamarin ya afku ne a yankin Ilepa da ke karamar hukumar Ifo ta jihar Ogun, da misalin karfe 8:00 na daren ranar Litinin, 5 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun kashe masallata 3 tare da sace wasu da dama a jihar Arewa

'Yan sanda sun kama wani da ya kashe makwabcinsa
Yadda Wani Mutum Ya Hallaka Makwabcinsa Saboda Akuya, Ya Shiga Hannun 'Yan Sanda Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Wani mazaunin garin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa akuyar mallakin marigayin ta shiga gidan Akinsanya sannan ta cinye doyar da ya busar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa lamarin ya fusata Akinsanya inda ake zargin ya kashe dabbar a kan haka.

Kan haka ne aka ce Ajibola ya fuskanci Akinsanya saboda abin da ya aikata wanda shine fada ya kaure a tsakaninsu inda shi kuma ya gayyaci ýan daba domin su farmaki mai akuyar.

Majiyar ta bayyana cewa Ajibola ya rasa inda kansa yake bayan harin sannan daga bisani ya mutu a asibiti.

Yadda lamarin ya faru, majiya

Mazaunin yankin wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda girman al'amarin ya ce:

"Ajibola na kiwon akuyoyi don tallafawa sana'arsa ta achaba. Da misalin karfe 4:00 na yamma ne daya daga cikin akuyoyinsa ta shiga gidan Akinsanya sannan ta ci masa doya da ya shanya.

Kara karanta wannan

"Ya dauki nauyin kawunnai na 10 zuwa Hajji": Tambuwal ya tuna haduwarsu ta karshe da Wigwe

"Da ya fito ya aga kuyar tana ci masa doya, sai ya kama ta ya yi mata duka har ta mutu.
"Tun da su makwabta ne a unguwa daya, sai Ajibola ya tunkare shi sannan ya kalubalance shi kan abin da ya aikata. Wannan ya haddasa zazzafan maganganu tsakaninsu, inda Akinsanya ya nemo ýan daba uku suka far masa.
"Yayin da suke dukansa, sai suka zuba masa barasa a kunnuwansa. Mazauna da suka gaggauta zuwa wajen sun same shi a kwance baya motsi sannan suka dauke shi zuwa asibitin Zion a Ilepa.
"Daga bisani aka mayar da shi asibitin jihar da ke Otta a rana na uku. Abin takaici, ya mutu a asibitin."

'Yan sanda sun kama wanda ake zargi

An tattaro cewa rundunar 'yan sanda sun kama wanda ake zargin, yayin da abokan aika-aikar nasa suka tsere suka bar garin.

Wani 'dan uwan marigayin da ya nemi a sakaya sunansa, ya yi zargin cewa 'yan sanda na kokarin rufe zancen.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan sanda suka kama masu laifi 400 a jihar APC

Da take tabbatar da lamarin, kakakin 'yan sandan jihar, Omolola Odutola, ta ce ana kokarin kama wadanda suka tsere, rahoton LIB.

Ta ce:

"An kama tare da tsare wanda ake zargin, Kolawole Akinsanya. Ana kokarin ganin an kama sauran da suka tsere."

An kama wani da ya kashe matashi a Kano

A wani labarin, mun ji cewa jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kano sun kama wasu mutane uku da ake zargin sun yi garkuwa tare da kashe wani yaro dan makwabcinsu mai shekaru 14.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdulahi Haruna Kiyawa, ya ce rundunar ta fara samun rahoto daga wani Alhaji Rabiu Abdullahi na Hotoron Fulani Quarters Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng