An gurfanar da uba da dansa kan yi wa 'yan sanda karyar garkuwa

An gurfanar da uba da dansa kan yi wa 'yan sanda karyar garkuwa

- Wani uba yayi yunkurin kubutar da dansa daga komar yan sanda bayan ya musu karyar yan bindiga sun yi garkuwa da dan

- Mutumin Wasiu Olugunju mai shekara 52 ya bawa yan sanda bayanin karya kan cewa anyi garkuwa da dan nasa Rilwan wanda yan sanda ke nema bisa zargin sata

- Uban da dan na shi sun shiga komar hukuma, kuma sun fara fuskantar shari'a sai dai sun karyata zargin yayin da kotu ta bada belin su kan kudi ₦500,000

Wani mutum mai shekara 52, Wasiu Olugunju, ya shiga komar yan sandan jihar Ondo bisa zargin bada bayanin bogi na garkuwa da dansa.

Wasiu, mai yaya uku, ya yaudari yan sanda da cewa yan bindigar da ba a san ko su waye ba sun yi garkuwa da dansa, Rilwan, don kar yan sandan su kama shi bisa tuhumar sa da sata.

An gurfanar da uba da dansa kan yi wa 'yan sanda karyar garkuwa
An gurfanar da uba da dansa kan yi wa 'yan sanda karyar garkuwa. Hoto: @daily_trust
Asali: Facebook

Dan sa, Rilwan Olugunju, shima ya shiga hannu bisa zargin satar kudi ₦538,133 daga wajen uban gidansa.

DUBA WANNAN: 'Yan Najeriya basu da shugaba mai tausayinsu, Kungiyar Dattawan Arewa

A bayanin tuhumar, wanda ake zargin sun aikata laifukan ranar 3 ga watan Oktoba, 2020 da misalin karfe 8:00 na safe a Shakina Venture, Oke Aro, Akure.

Dan sanda mai gabatar da kara, Sgt. Augustine Omhenimhen, ya shaidawa kotu cewa wanda ake kara na farko, Wasiu, ya bawa yan sanda bayanin karya akan an sace dansa don kar yan sanda su kama shi.

Omhenimhen ya sake karanto cewa wani mutum Aremu Musa Adebiyi bisa zargin satar nasa kudi, a Shakina Venture kafin daga bisani ya boye.

Mai gabatar da kara ya ce Wasiu ya yaudari yan sanda kan cewa dansa, Rilwan, wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun yi garkuwa da shi, saboda kar yan sanda su kama shi.

KU KARANTA: Idan Boko Haram sun gama da Arewa, za su tunkari Kudu, Aisha Yesufu

Ya ce laifin ya sabawa sashe na 125A, 390(6), 516(B) da kuma 519 na dokar manyan laifukan jihar Ondo na shekarar 2006.

Sai dai wanda ake zargin basu amsa laifukan guda hudu da ake zargin su da su ba.

Lauyan da ke kare su, Mr Femi Akintoye, ya bukaci a bada su beli akan wasu sharudda.

Mai shari'a O. R Yakubu ya bada su beli akan kudi ₦500,000 tare da mutum daya wanda zai tsaya musu.

A wani labarin, gwamnatin tarayyar Najeriya, a ranar Lahadi ta ce shirin samar da ayyuka na musamman, SPW, guda 774,000 zai fara ne a ranar 5 ga watan Janairun shekarar 2021.

Karamin ministan Kwadago da samar da ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ne ya shaidawa The Nation hakan ranar Lahadi a Abuja.

Shirin samar da ayyukan ga masu sana'o'in hannu na watanni uku inda za a rika biyansu N20,000 duk wata ya samu tsaiko sakamakon rashin jituwa tsakanin ministan da tsohon shugaban hukumar samar da ayyuka ta kasa, NDE, Nasir Ladan da Buhari ya sallama daga aiki makon data gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164