Tsadar rayuwa: Tinubu Ya Ki Karbar Shawarar Bude Iyakoki da Kayyade Farashin Abinci

Tsadar rayuwa: Tinubu Ya Ki Karbar Shawarar Bude Iyakoki da Kayyade Farashin Abinci

  • Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ba ta gamsu da tsarin bude iyakokin da nufin abinci ya zo daga kasar waje ba
  • Shugaban Najeriyan yana ganin hakan ba zai taimakawa manoma ba kuma wasu za a budewa harkar cutar jama'a
  • Gwamnatin tarayya ta kuma yi watsi da shawarar kafa hukumar da za ta kayyade kudin kayan abinci a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya yi fatali da kiran masu kira na cewa kyau a shigo da abinci daga kasashen waje domin a samu sauki.

A jawabin bayan taron da aka samu daga ofishin Bayo Onanuga, an fahimci Bola Tinubu zai cigaba da tafiya a kan tsarin da ake kai.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya samu babban mukami, kungiyar AU ta ba shi nauyi a nahiyar Afrika

TINUBU
Shugaba Bola Tinubu da Gwamnoni a Aso Rock Hoto: @TheTope_Ajayi
Asali: Twitter

Taron shugaban kasa Tinubu da Gwamnoni

Shugaban kasa ya hadu da gwamnonin jihohi da Ministan Abuja domin tattauna yadda za a magance matsalolin yunwa da kunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya nanatawa Najeriya cewa gwamnatinsa da gaske take yi wajen ganin ‘yan kasa sun noma isasshen abincin da za a ci.

Shugaban Najeriyan yana neman mafita a cikin gida domin kawo karshen matsalar abinci, tsare-tsaren da Atiku Abubakar ya soka.

Yadda Tinubu zai magance rashin abinci

Daga cikin matakan da The Cable ta ce an dauka akwai inganta noma sannan sai a guji shigo da kayan abinci daga kasashen ketare.

Tinubu ya ce idan aka bada damar kawo abinci daga kasashen waje, wasu ‘yan kasuwa sun samu hanyar yin cuwa-cuwa a kasar.

A maimakon a yi kokari samar da abincin da al’umma za su ci, shugaban kasar ya ce wasu ne za a budewa hanyar samun kazamar riba.

Kara karanta wannan

Aiki na Kyau: Dalilin Shugaba Tinubu na ware Abba, ya jinjina masa cikin Gwamnoni

A jawabinsa, shugaba Tinubu ya nuna bai goyon bayan kayyade farashin kaya kuma ya ce sai jihohi sun dage game da sha’anin kiwo.

Shugaba Tinubu zai bude iyakoki?

“Ba zan kirkiri hukumar kula da farashi ba, kuma ba zan amince a shigo da abinci ba.”
“A madadin haka, za mu taimakawa manomanmu da tsare-tsaren da za su taimaka masa wajen samun karin abinci a kasa.”

- Bola Tinubu

Muhsin Gambo Lawal ya shaidawa Legit cewa idan kasa ta gagara noma isasshen abincin da ake bukata, dole a nemo daga kasashen waje.

Shugaban shirin na STAPIN ya ce abubuwa da-dama sun yi sanadiyyar karancin abinci; rashin tsaro, sauyin yanayi, tsadar kaya da talauci.

Muddin ba a yaye wadannan matsaloli ba, zai yi wahala Najeriya ta noma abin da za ta ci, idan aka yi sake hakan zai tilasta bude iyakokin kasar.

Muhsin kwararre ne wajen wayar da kan manoma, ya yi aiki da kamfanonin Miagro, Interrproduct Link, Croplife Africa da Adama W/Africa.

Kara karanta wannan

Muhimman matakai 6 da aka dauka da Tinubu ya zauna da Gwamnoni a Aso Villa

Bola Tinubu ya yabawa Abba a Kano

Ana da labarin yadda Shugaban kasa ya yabi kokarin da Abba Kabir Yusuf ya fara a jihar Kano na yakar masu boye kayan abinci.

Abba Kabir Yusuf bai je taron da shugaban kasa ya yi da gwamnoni ba, Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya wakilci gwamnan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng