Tsadar Rayuwa: Yan Kasuwar Hatsi a Kano Sun Karya Farashin Kayan Abinci Don Saukakawa Jama’a
- A wani labari mai dadin ji, 'yan kasuwa a Dawanau, jihar Kano sun sanar da karya farashin kayan hatsi don ragewa al'umma radadi
- Shugaban kungiyar raya kasuwar Dawanau a Jihar Kano, Alhaji Muttaka Isah ya ce matakin karya farashin zai kuma jawo ciniki mai yawa
- A yanzu dai farashin hatsi irin su shinkafa, wake, gero, dawa, da sauran su sun koma dai dai aljihun mutane kamar yadda Legit ta tattara a kasa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Kano - Dillalan hatsi a kasuwar hatsi ta kasa da kasa ta Dawanau a jihar Kano sun karya farashin hatsi domin rage radadin da jama'a ke fuskanta a jihar.
Tsadar kaya: Tsohon hadimin Buhari ya magantu yayin da gwamnatin Tinubu ta rufe babban kanti a Abuja
Shugaban kungiyar raya kasuwar Dawanau a Jihar Kano, Alhaji Muttaka Isah ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba.
Ya ce matakin da kungiyar ta yanke na karya farashin zai kuma jawo ciniki mai yawa, yayin da 'yan kasuwar ke fama da rashin ciniki a 'yan kwanakin nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Alhaji Isah:
“Idan ka zaga kasuwa a yanzu, za ka ga an rage farashin hatsi irin su masara, dawa, gero da wake, sabanin farashin su na baya."
Sabon farashin kayan hatsi a kasuwar Dawanau
Alhaji Isah ya yi bayani game da sabon farashin kayan hatsi a kasuwar yanzu, kamar yadda Arise TV ta ruwaito.
Masara:
Yanzu haka ana sayar da buhun masara akan naira dubu 53 sabanin tsohon farashin naira dubu 60.
Dawa:
Yanzu dai ana sayar da buhun Dawa a kan naira 49,000, sabanin farashin da aka sayar da shi a baya kan naira 55,000.
Gero:
Haka kuma, buhun gero da a da ake sayen shi akan naira 60,000, yanzu ya koma naira 53,000.
Wake:
Farashin wake a yanzu yana kai naira 85,000 zuwa naira 90,000, sabanin tsohon farashin naira 95,000 zuwa naira 100,000, gwargwadon kyawun sa.
Waken soya:
Buhun waken soya yanzu ana sayar da shi akan naira 65,000, sabanin naira 68,000 a da.
Shinkafar gida:
A baya ana sayar da babban buhun shinkafar gida tsakanin naira 110,000 zuwa N115,000, amma yanzu ta koma tsakanin naira 95,000 zuwa naira 100,000.
An yi kira ga gwamnati ta tallafawa manoma
Radio Nigeria ta ruwaito shugaban kungiyar 'yan kasuwar ya bayyana cewa sayar da kayan abinci a kasuwa ya ragu saboda halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da tallafin taki da sauran kayayyakin amfanin gona ga manoma domin samun wadatar abinci.
Kasuwar hatsi ta kasa da kasa ta Dawanau ita ce mafi girma a yammacin Afirka, inda ake samar da kayayyaki ga kwastomomi a Najeriya, Nijar, Chadi, Kamaru da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, da dai sauransu.
Gwamnati ta dauki matakin karya farashin kayan abinci
A wani labarin makamancin wannan, Legit Hausa ta ruwaito cewa ita ma gwamnatin tarayya ta sanar da shirin karya farashin kayan abinci.
Gwamnatin ta ce za ta fitar da ton dubu 42 na nau'ikan kayan abinci domin tabbatar da cewa abincin ya wadata wanda zai tilasta saukar farashin sa a kasuwanni.
Tun bayan janye tallafin man fetur, da karya darajar Naira, tsadar rayuwa ta mamaye Najeriya, sakamakon hauhawar farashin kayan abinci da na masarufi.
Asali: Legit.ng