Gwamnatin Tinubu Za Ta Raba Kayan Tallafi Ga Talakawan Najeriya, Minista Ya Yi Karin Bayani
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana kokarin kawo karshen tsadar rayuwa da wahalhalun da al'umma ke ciki a kasar
- Gwamnatin Tinubu ta kammala shiri tsaf don raba kayan tallafi kyauta ga mabukata da talakawa a fadin kasar
- Ministan noma da tsaron abinci, Abubakar Kyari ya tabbatar da hakan inda ya ce talakawa ne kawai za su samu tallafin ba tare da su biya ko sisi ba
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta raba tallafin kayan hatsi ga talakawan Najeriya, Abubakar Kyari, ministan noma da tsaron abinci ya bayyana.
Kyari ya bayyana hakan ne daga kokarin da gwamnatin Tinubu ke yi na rage yunwa da wahalar da ake sha a kasar, jaridar Vanguard ta rahoto.
Su wanene za su ci gajiyar kayan tallafin?
Ministan ya ce an tanadi kayayyaki da matakan da suka dace don kara tabbatar da ganin cewa mabukata ne kawai suka samu tallafin abinci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Arise News ta ruwaito cewa, Kyari ya bayyana cewa gwamnati ta yi imanin cewa hauhawar farashin kayan abinci ya samo asali ne saboda karfin bukata a kasuwa da wadatar kaya.
Ya kara da cewa matsalar iya siyan kayan shine babban kalubalen da 'yan Najeriya ke fuskanta, ba batun samar da kayayyaki ba.
Ya yi magana ne a ranar Laraba, 14 ga watan Fabrairu, a wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
Jawabin ministan noma a taron manema labarai
Kyari ya ce:
"Musamman, sauran ayyukan shiga tsakani da muke dubawa shine rumbun ajiyar kayan hatsi, yanzu haka muna da metric tan 53,000 na hatsi a rumbun ajiyarmu.
"A ma'ajiyarmu a fadin kasar, mun bukaci a saki metric tan 42,000, saboda kyakkyawan dalili, muna bukatar sauran metrin tan 11,000 saboda abin da ka iya tasowa.
"Don haka, ana shirin fitar da 42,000 kuma muna jiran alkaluma ne, haka kuma muna tattaunawa da hukumar NEMA don mu kai hatsin inda aka fi bukatar su.
"Za a bayar da hatsin ga mabukata a kyauta, za su same shi babu ko sisi."
Martanin 'yan Najeriya kan rabon kayan da gwamnati za ta yi
Malam Abubakar Gawu ya ce:
"Bana tunanin wannan zai kawo mafita ga halin da ake ciki a yanzu don an saba irin haka, ka ji an ce an bayar da kayan tallafi amma talaka ba zai gani a kasa ba, wadanda aka baya kayan sune suke babakere a kai."
Malama Asiya kuwa cewa ta yi:
"Da ace kayan abincin zai isa ga wadanda suka fi bukata ne da an samu sauki, ba wanda mutum zai je karbar kayan tallafi a hada shi da mudun shinkafa daya ko biyu ba. Kwana nawa mudun shinkafa biyu zai yi wa mutum? Ka ga ana cinyewa za a sake komawa gidan jiya ne.
"Ya kamata gwamnati ta duba hanyar da za a samu maslaha mai dorewa ba na wucin gadi ba. Talaka na cikin wani hali hatta masu rufin asirin ma suna ji a jikinsu, babu ranar da za ka shiga kasuwa baka ji an yi karin kudin kaya ba.
Gwamnan Ogun zai raba kayan tallafi
A wani labari makamancin wannan, gwamnatin jihar Ogun ta bayyana aniyarta na fara aiwatar da wani shiri na naira biliyan 5 domin ragewa al'umma radadin halin da ake ciki na matsin tattalin arziki.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa Gwamna Dapo Abiodun, ne ya sanar da hakan a yammacin ranar Laraba, 14 ga watan Fabrairu a wani taron manema labarai na gaggawa a cibiyar labarai ta Olusegun Osoba da ke ofishin gwamna na Oke Mosan.
Asali: Legit.ng