‘Yan Bindiga Sun Saba Lalata da Matanmu da Rana Babu Yadda Aka Iya – ‘Yan Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Saba Lalata da Matanmu da Rana Babu Yadda Aka Iya – ‘Yan Zamfara

  • Mutanen da ke kauyukan karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara sun tsere saboda matsalar rashin tsaro
  • Akwai wuraren da sun koma rayuwa tare da ‘yan bindiga, an manta da labarin jami’an 'yan sanda ko sojoji
  • Miyagu suna shigowa gidajen mutane da rana, su yi ta’adi ga matan aure da ‘yan mata a kauyuka da karfin tsiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Zamfara – Rahotanni sun shaida cewa hare-haren da ake kai wa a kauyukan Zamfara yana cigaba da yin muni da canza salo.

BBC Hausa ta ce yanzu ‘yan bindiga sun koma yin fyade ga ‘yan mata da matan aure a gidajen mazaje da iyayensu a yankin Tsafe.

'yan bindigan Zamfara
Jami'an tsaro da za su yaki 'yan bindigan Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Baya ga kashe-kashe, karbar kudin fansa da lalata dukiya da miyagun ‘yan bindigan suke yi, al’umma na kukan ana lalata da mata.

Kara karanta wannan

Tsadar Rayuwa: An bukaci Shugaba Tinubu ya gaggauta yin murabus, karin bayani ya bayyana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana ta tserewa daga kauyuka a Zamfara

Wani da aka yi hira da shi a gidan rediyon ya bada labari 70% na mutanen kauyukansu sun tsere a dalilin wannan masifa.

A cewar wannan Bawan Allah, da farko ‘yan bindigan su kan shigo gari ne su tsere da dabbobi kuma yi suyi garkuwa da mutane.

Yanzu kuwa miyagun su na zuwa da rana tsaka, kuma su yi ta zama har tsakar dare.

'Yan bindiga suna yi wa mata fyade

Kiri-kiri ‘yan bindigan su ke yawo a kauyuka dauke da kayan sojoji da makamai, ta kai su na shiga gidaje su yi wa mata fyade.

Duk macen da ta nemi tayi masu gardama kuwa, kashinta ya bushe domin za ayi gaba da ita zuwa jej ayi duk abin da aka ga dama.

Sai bayan kwanaki biyu, uku ko hudu sannan iyalin wannan mata ko yariniya za su gan ta.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mahara sun hallaka jami'an 'yan sanda 2 da sace fiye da 40 a sabon hari a Zamfara

Ina jami'an tsaro a Zamfara?

Lamarin ya yi munin da ta kai an yi shekaru fiye da 10 ba a turo ‘dan sanda zuwa wannan wuri ba, doka tana hannun ‘yan bindiga.

Vanguard ta tabbatar da rahoton, ta ce ana karbar kudi daga hannun manoma kafin ‘yan bindigan su bada dama a girbe kayan gona.

Gwamnatin jihar Zamfara ta bakin kakakin gwamna, Sulaiman Bala Idris ta ce ana neman yadda za a kawo karshen tashin hankalin.

An yi tsit 'yan bindiga na ta'adi a Zamfara

Abba Hikima wanda lauya ne mai kare hakkin al’umma ya rubuta a Facebook:

"Da alamu ʼyan Nigeria sun fara yanke ƙauna da ƙasar nan."
"Ɗazu da safe na saurari wani labarin BBC Hausa mai tayar da hankali a kan yadda ʼyan bindiga suke cin zarafin jama’a da matan aure da tsakar rana a wani ƙauye dake karamar hukumar Tsafe da ke Zamfara."

- Abba Hikima

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun shiga jimamin rashin da Super Eagles ta yi a wasan AFCON 2023, ga martaninsu

Askarawa sun fara aiki a Zamfara

Ana da labari an zargi jami’an sabuwar rundunar tsaro da aka kaddamar a Zamfara da kashe na kusa da Sanata Kabir Garba Marafa.

Tsohon Sanatan ya sha alwashin maka Asakarawan a kotu a kan mutuwar wannan Bawan Allah da yake ganin bai yi laifin komai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng