Kano: An Bai Wa Gwamna Abba Shawara Kan Rushe Masarautun Kano
- Wata kungiya ta al’ummar Rano, Kibiya da Bunkure ta aika muhimmin bukata a gaban gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
- Kungiyar ta roki Abba Gida Gida da ya yi watsi da duk wani yunkuri na rushe karin masarautu hudu da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kafa a jihar
- Shugaban kungiyar, Wali Ado Rano, ya yi ikirarin cewa mutanen Kano na goyon bayan barin masarautun a yadda suke a yanzu
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Kano - Wata kungiyar ci gaban al'ummar Rano, Kibiya da Bunkure, ta roki gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da ya yi watsi da duk wani yunkuri na rusa sabbin masarautu biyar da aka kafa a jihar.
Ku tuna cewa, tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kafa karin masarautu hudu da suka hada da Rano, Karaye, Bichi da Gaya, baya ga masarautar Kano.
Shin mutanen Kano na goyon bayan barin masarautun?
Da yake jawabi ga menama labarai a garin Kano, shugaban kungiyar, Wali Ado Rano, ya yi ikirarin cewa mai akasarin mutanen Kano suna son dorewar wadannan masarautun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
"Ya kamata mu bayyana karara cewa dorewar wadannan masarautu yana da goyon bayan yawancin mutanen yankinmu.
"Abu na biyu, dorewar wadannan masarautu ba yana nuin jefa masarautar Kano a wani yanayi bane kamar yadda wasu ke gani.
"Saboda haka, alakarmu ta 'yan uwantaka za ta ci gaba da wanzuwa tsakanin mutanen sabbin masarautun da na masarautar Kano."
Barin masarautun zai kawo karin ci gaba a jihar, Rano
Mista Rano ya bayyana cewa, daukaka darajar sarakunan gargajiya ba sabon abu bane a Najeriya.
Ya ci gaba da cewar kara girman hakimai zuwa na gudunmomi zuwa sarakuna ya samo asali ne tun daga lokacin Jihadin Fulani har zuwa yau.
Ya ce dorewar masarautun zai ba da damar da karin garuruwa za su samu ci gaba wanda hakan ya rage yanayin cunkoso a cikin birnin Kano.
Daga karshe, Mista Rano ya bukaci jama'a da su kara kaimi wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.
Legit Hausa ta tuntubi wasu Kanawa don jin ta bakinsu kan a bar masarautun ko a rushe su.
Abban Sanka ya ce:
"A ganina barin wadannan masarautu zai fi kyautuwa musamman ko don saboda ci gaban jiharmu. Misali daga lokacin da aka kafa masarautun Bichi, Karaye da sauransu an samu tarin ci gaba sosai a wadannan yankuna.
"Idan har za a cire son zuciya babu ta inda wadannan masarautu suka rage darajar gidan sarautar Kano har gobe tana nan a inda take babu abin da ya sauya.
"Ina kira ga Gwamnanmu Abba Kabir Yusuf da ya bar abubuwa yadda suke ya mayar da hankali kan ayyukan ci gaba da yake yi mana. Allah kuma ya taimake shi."
Mallam Labaran na Gandun Albasa kuwa cewa ya yi:
"A wannan yanayi da ake ciki a kasar yanzu, babban abin da ya kamata a mayar da hankali a kai shine yadda rayuwar talakawa za ta inganta ba batun masarautun Kano ba.
"A bar su yadda suke tun da babu wani koma baya da hakan ya kawo a jihar illa ma ace ci gaba muka samu, saboda wasu yankunanmu na karkara da a baya ba'a jin su sun samu wani ci gaba da kafuwar wadannan masarautu.
"Abu mafi ahla a bar su sannan a mayar da hankali wajen inganta rayuwarmu mu talakawa a jihar. Wannan shine abin da muka fi bukata a yanzu."
Tsohon hadimin Ganduje ya magantu kan masarautar Kano
A wani labarin, mun ji a baya cewa Garba Kore tsohon hadimin Abdullahi Umar Ganduje ya yi tsokaci kan batun masarautun jihar Kano.
A wata hira da aka yi da shi, Alhaji Garba Kore, ya bayar da shawarar a maida masarautar Kano yadda ta ke kafin 2019.
Asali: Legit.ng