Majalisar Dattawa Ta Sanya Labule da Hafsoshin Tsaro, Bayanai Sun Fito
- Majalisar dattawan Najeriya na wata ganawar sirri da shugabannin hukumomin tsaro da tawagar tattalin arziƙi kan kalubalen tsaro da ake fuskanta a ƙasar nan
- Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele, ya gabatar da ƙudirin da majalisar ta amince da shi domin shiga ganawar ta sirri
- Taron na sirri ya samu halartar hafsoshin tsaro da mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu da wasu ministoci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - A halin yanzu majalisar dattawa tana wata ganawar sirri da hafsoshin tsaron ƙasa, kan matsalar rashin tsaro a zauren majalisar da ke birnin tarayya Abuja.
Hafsoshin tsaron da majalisar ke ganawa da su sun haɗa da, babban hafsan tsaro na ƙasa, Christopher Musa, shugaban hukumar sojin ƙasa, Taoreed Lagbaja, shugaban hukumar sojin sama, Air Marshal Hasan Bala Abubakar, cewar rahoton The Nation.
Sauran sun haɗa da shugaban hukumar sojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla, sufeto janar na ƴan sanda, Kayode Egbetokun da kuma babban daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Yusuf Magaji Bichi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tattaro cewa, mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribadu, ministan kuɗi da tattalin arziki, Dr Olawale Edun, ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, darakta janar na hukumar leken asiri ta ƙasa (NIA), Ahmed Rufai Abubakar, na cikin mahalarta taron.
Sauran mahalarta taron sun haɗa da ministan harkokin cikin dida, Hon. Olubunmi Tunji-Ojo, ministan harkokin ƴan sanda, Ibrahim Geidam da ƙaramar ministar harkokin ƴan sanda, Imaan Sulaiman-Ibrahim.
Meyasa aka shiga ganawar sirrin?
Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele, ya gabatar da ƙudirin da neman shiga ganawar sirri, domin karɓar bayanan tsaro, cewar rahoton jaridar The Punch.
Bayan haka, sanatocin da shugabannin hukumomin tsaro da na tattalin arziƙi daban-daban sun shiga wani zama na sirri bayan da majalisar ta amince da ƙudirin Bamidele.
An Rantsar da Sabbin Sanatoci 3 a Majalisa
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya jagoranci rantsar da sabbin sanatoci uku a zaman majalisar na ranar Talata, 13 ga watan Fabrairu.
Sabbin sanatocin da aka rantsar a zauren majalisar sun haɗa da Prince Pam Mwadkon (ADP, Plateau ta Arewa) da Farfesa Anthony Ani (APC, Ebonyi ta Kudu).
Asali: Legit.ng