Muhimmin Dalilin 1 da Ya Sa Ivory Coast Ta Doke Najeriya a Wasan Ƙarshe Na Kofin AFCON

Muhimmin Dalilin 1 da Ya Sa Ivory Coast Ta Doke Najeriya a Wasan Ƙarshe Na Kofin AFCON

  • Koci Jose Peseiro ya bayyana muhimmin dalilin da ya jawo Najeriya ta sha kashi a hannun tawagar ƴan wasan Ivory Coast a wasan ƙarshe na AFCON
  • Mai horarwan ya ce tawagar ƴan kwallon Najeriya sun yi iya bakin ƙoƙarinsu amma a wasan Ivory Coast ta fi su taka leda mai kyau
  • A cewar Peseiro, ɗan asalin ƙasar Portugal, a wasu lokutan mutum zai so ya yi wani abu amma kuma sai ya tsincii a kansa a yanayin da ba zai iya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abidjan, Côte d’Ivoire - Mai horar da tawagar ƴan wasan Super Eagles, Jose Peseiro, ya aminta cewa ƴan wasan Ivory Coast sun nuna bajinta a wasan ƙarshe da aka buga ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Atiku da Obi sun aike da sako mai muhimmanci kan rashin nasarar Super Eagles a wasan karshe na AFCON

Ƙocin ya bayyana cewa tawagar ƴan wasan ƙasa mai masaukin baƙi sun fi ƙarfin Najeriya a wasan ƙarshen da aka yi na gasar kofin nahiyar Afirka (AFCON) a birnin Abidjan.

Kocin Najeriya, Jose Peseiro.
AFCON 2023: Dalilin da ya sa Ivory Coast ta doke Najeriya, Ƙocin Super Eagles Hoto: Daniel Beloumou Olomo
Asali: Getty Images

Legit Hausa ta rahoto cewa Sébastien Haller ne ya zura kwallo mintuna kaɗan kafin a hura tashi wanda ya bai wa ƙasar Ivory Coast damar doke Najeriya da ci 2-1.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haller ya leƙa zaren Najeriya a minti na 81 da fara wasan bayan Frank Kessie ya rama ta farko a mintuna 62 a wasam da aka ɓarje gumi ranar Lahadi, 11 ga watan Fabrairu.

Wannan shi ne karo na uku da Ivory Coast ta jijjiga kofin AFCON bayan nasarar da ta samu a 1992 da 2015, duk a bugun daga kai sai mai tsaron raga, rahoton BBC.

Meyasa Najeriya ta yi rashin nasara?

Kara karanta wannan

Najeriya vs Cote d'Ivoire: Malamin da ya yi hasashen nasarar Tinubu, ya yi magana kan Osimhen

Kamar yadda jaridar labaran ƙwallo Goal ta rahoto, kocin ƴan wasan Najeriya ya ce:

"Ivory Coast ta fi ƙarfin mu a yau. Ban ji daɗin (wannan rashin nasara) ba haka ma tawagar ƴan wasa na sun yi takaici, amma a wurina, ina ganin sun yi iya bakin kokarinsu.
"Wani lokoacin zaku ga kuma da burin yin wani abu amma ku gaza, haka wasa yake."

A halin da ake ciki dai ana sa ran Super Eagles za ta dawo Najeriya ko dai a yau Litinin 12 ga watan Fabrairu ko kuma ranar Talata 13 ga watan Fabrairu, 2024.

Atiku da Obi sun yi magana

A wani labarin kun ji cewa Atiku Abubakar da Peter Obi sun mayar da martani daban-daban kan rashin nasarar Super Eagles a wasan ƙarshe na AFCON 2023.

Ivory Coast ta doke Super Eagles ta Najeriya a ranar Lahadi a wasan ƙarshe na AFCON 2023, inda ta lashe gasar, Najeriya ta zo matsayi na biyu

Asali: Legit.ng

Online view pixel