Tsadar Rayuwa: Gwamnan Arewa Ya Sharewa Iyalai 70,000 Hawaye, Ya Raba Kayan Abinci Na Miliyan 225

Tsadar Rayuwa: Gwamnan Arewa Ya Sharewa Iyalai 70,000 Hawaye, Ya Raba Kayan Abinci Na Miliyan 225

  • Gwamnan Bornmo, Farfesa Babagana Zulum ya gwangwaje al'ummar yankin Bama da ke jihar da sha tara ta arziki
  • Yayin da ake fama da tsadar rayuwa a kasar, Gwamna Zulum ya rabawa gajiyayyu kayan abinci da farashinsa ya kai naira miliyan 225
  • Mutanen da suka ci gajiyar wannan rabo sun kasance wadanda harin ta'addancin Boko Haram ya ritsa da su

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi rabon kayan abinci da farashinsu ya kai naira miliyan 225 ga iyalai sama da 70,000 a karamar hukumar Bama ta jihar.

An raba wa iyalai marasa gata kayayyakin ne a ranar Litinin, 12 ga watan Fabrairu, yayin da ake tsaka da fama da tsadar rayuwa a kasar.

Kara karanta wannan

AFCON: Ana saura kwana 4 aurensa ya rasu, cewar iyalan marigayi Ayuba a Kwara, bayanai sun fito

Gwamna Babagana Zulum ya yi rabon kayan abinci
Tsadar Rayuwa: Gwamnan Arewa Ya Sharewa Iyalai 70,000 Hawaye, Ya Raba Kayan Abinci Na Miliyan 225 Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

Gwamna Zulum ya rabawa gajiyayyu kayan abinci

An raba kayan abincin ne lokacin da gwamnan ya ziyarci yankin don tattaunawa da jami'an tsaro kan hanyar da ta dace a bi don inganta zaman lafiya a yankin, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zulum ya ce an raba kayan abinci da kudade ne domin tallafawa al'umman da hare-haren ta'addanci ya ritsa da su da kuma hana mayakan Boko Haram daukar mutanen a cikinsu.

Ya ce:

"Wannan yana daga cikin kokarin da muke ci gaba da yi na samar da tallafi ga marasa gata a Bama wadanda rikicin Boko Haram ya shafa da karancin abin rayuwa."

Jimillar mata 45,000 ne suka samu tsabar kudi N5000 da turmin zani daya kowannensu, yayin da kowani iyali ya samu N25,000 da buhun shinkafa da na masara.

Gwamna Zulum zai rage kudin fetur

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnatin Kano ta cika alkawari, ta dira kan rumbun ajiyar masu boye abinci

A gefe guda, Legit Hausa ta kawo a baya cewa Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya yi alkawarin rage kudin man fetur ga manoma a jihar.

Zulum ya ce zai rage farashin mai din ne musamman don manoman Damasak da ke karamar hukumar Mobbar a jihar, cewar BusinessDay.

Gwamnan ya ce ya dauki matakin ne don inganta samar da abinci a jihar yayin da yankin ya sha fama da matsalar rashin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng