Bidiyon magidanci da ya sheƙe abokinsa bayan ya yi mafarkin ya kwanta da matarsa

Bidiyon magidanci da ya sheƙe abokinsa bayan ya yi mafarkin ya kwanta da matarsa

  • Magidanci mai suna Kwadwo Adusei ya sheke abokinsa har lahira bayan ya yi mafarkin ya kwanta da matarsa ta aure
  • Daga nan Adusei ya kai wa kakansa farmaki kan zarginsa da satar mazantakarsa, lamarin da yasa ya kasa haihuwa
  • A yadda Adusei ya sanar da manema labarai, mafarkinsa na zama gaskiya, shiyasa ya hanzarta dakile faruwar wannan

Ghana - Wani magidanci mai shekaru 45 mai suna Kwadwo Adusei wanda aka fi sani da Desco, ya shiga hannun jami'an tsaro kan halaka abokinsa a Wawaase da ke Afigya Kwabre ta kudu a yankin Ashanti na kasar Ghana.

Wanda ake zargin ya sheke abokinsa ne bayan ya yi mafarkin cewa ya kwanta da matarsa, shafin LIB suka wallafa.

Bidiyon magidanci da ya sheƙe abokinsa bayan ya yi mafarkin ya kwanta da matarsa
Bidiyon magidanci da ya sheƙe abokinsa bayan ya yi mafarkin ya kwanta da matarsa. Hoto daga lindaikejisblog.com
Source: UGC

An gano cewa ya yaudari marigayin mai shekaru 48 mai suna Kwesi Banahene zuwa daji inda ya soka masa wuka sau da yawa a sassan jikinsa.

Read also

Kudajen zuma sun dinga harbin wani mutum yayin da ya ke turmi da tabarya da matar aure

Daga bisani an tsinci gawar mamacin a daji bayan an tura masu nema neman shi sakamakon batan da ya yi na kwanaki.

Makashin an gano ya yi yunkurin sheke kakansa bayan kashe abokinsa da yayi. Daga bisani ya zargi kakansa da sace masa mazantaka, lamarin da yasa ya kasa haihuwa.

Kakansa ya tsallake farmakin kuma a halin yanzu ya na asbiti Ankaase inda ake kula da shi.

Desco ya sanar da manema labarai cewa, shi sau da yawa mafarkinsa na zama gaskiya kuma ba zai iya jira ya ga wannan ya zama gaskiya ba, wanda hakan yasa ya yi hanzarin daukar mataki.

Kudajen zuma sun dinga harbin wani mutum yayin da ya ke turmi da tabarya da matar aure

A wani labari na daban, wani mutum daga kauyen Kwaramba a garin Gokwe na kasar Zimbabwe ya sha harbin kudajen zuma yayin da ya ke kwance turmi da tabarya da matar aure.

Read also

Manyan ƴan siyasan arewa 5 da suka yi rantsuwar ba za su sauye sheƙa ba amma suka saɓa

Kamar yadda LIB suka ruwaito, an tattaro cewa Jethro Maimba ya labe a daji inda ya kwanta da Lizzie Maphosa yayin da al'amarin ya faru.

Mijin Maphosa mai suna Joseph Musariri an gano cewa ya ja kunnen Maimba sau babu adadi kan ya daina kwanciya da matarsa. Daga nan ne ya yi tsinuwa kan matarsa wacce kuwa ta bi su.

Source: Legit

Online view pixel