Sojan ruwa ya sokawa sojan sama wuka bayan ya kama shi turmi da tabarya da matarsa

Sojan ruwa ya sokawa sojan sama wuka bayan ya kama shi turmi da tabarya da matarsa

- Wani sojan ruwa dan Ghana mai suna Umar yana daure a sansanin sojin ruwa dake Sekondi sakamakon datsar wani Benard da yayi

- Kamar yadda aka samu labari, ya sokawa Benard wuka a gadon bayansa ne bayan ya kama shi yana lalata da matarsa a gadonsu na sunna

- Ofishin 'yan sanda sun kama Umar ne bayan ya je kai korafi a kan Benard wanda ya cije shi a dan yatsa yayin da ya kama shi suna lalatar

Sansanin sojin ruwa na Sekondi sun rike wani sojan ruwa na Ghana mai suna Leading Seaman Umar Sahid Abubakar a kan datsar wani Benard Ababio, sojan sama, bisa kama shi yana lalata da matarsa.

Sojan ruwan yana aiki ne da Eastern Naval Command, wanda ya dauki wuka ya datsi kumatu da kwankwason Benard Ababio bayan ya kama shi turmi da tabarya yana lalata da matarsa Linda Akosua Buabeng a kan gadonsu na sunna a Ketan.

Ofishin 'yan sandan Sekondi sun kama Sahid Abubakar ne yayin da yaje kai korafi akan Benard bisa cizon shi da yayi a dan yatsa yayin da ya kama shi yana lalatar.

KU KARANTA: Ba a zabe ni domin biyan albashin ma'aikata ba, Gwamna El-Rufai

Sojan ruwa ya sokawa sojan sama wuka bayan ya kama shi turmi da tabarya da matarsa
Sojan ruwa ya sokawa sojan sama wuka bayan ya kama shi turmi da tabarya da matarsa. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

An kama shi ne bayan isowar Benard wanda shima yaje kai korafi ofishin 'yan sanda akan datsar shi da aka yi.

Pulse Ghana sun bayyana abubuwan da suka samu a hannunsa kamar farar singileti, wanduna na jeans guda biyu, wanduna na auduga guda biyu, riga, agogo, canvass, man wanke hakora da kuma wani AV cable na sojojin sama.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan ta'adda na shirin kaiwa filayen jiragen sama farmaki, FG

A wani labari na daban, yayin da kasar Saudi Arabia ta sanar da cewa ba a samu ganin watan Ramadan ba ranar Lahadi, Mai alfarma Sarkin Musulmi ya bukaci 'yan Najeriya su fara duban jinjirin watan Ramadan a ranar Litinin.

Wannan lamarin ya janyo cece-kuce daga jama'a da dama, sai dai Legit.ng ta samu zantawa da Shehin Malami Ustaz Abu Jabir wanda aka fi sani da PenAbdul.

Malamin ya bayyana cewa kasar nan tana la'akari da ganin watanmu ne ba kasar Saudia ba. Koda kasar Saudi Arabia tace bata ga wata ba, Najeriya za ta duba watan, idan duk ba a gani ba, toh an yi tarayya a rashin ganin watan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng