Dumu-dumu: Hukumar makaranta ta kama 'yan aji 4 na sakandare suna lalata a kungiyance

Dumu-dumu: Hukumar makaranta ta kama 'yan aji 4 na sakandare suna lalata a kungiyance

- An dakatar da dalibai 20, yan aji hudu na Sakandare, sakamakon kama su da laifin taruwa suna lalata

- Kamar yadda rahoton yazo, an kama daliban, maza da mata, a wurin kwanan yara mata dake makarantar Loreto a Zimbabwe

- An kamasu suna lalata, tsirara haihuwar iyayensu, kamar yadda rahotanni suka iso wurin ma'aikatar ilimi ta Zimbabwe

An dakatar da dalibai 20 'yan aji 4 da ke babbar makarantar sakandire ta Loreto a Zimbabwe sakamakon kamasu da laifin lalata da juna a watan Yuli.

Da yake makarantar ta maza da mata ce, an kama daliban tsirara suna lalata a inda yara matan ke kwana na makarantar da ke Silobela, yayin da suke shirin fara jarabawar watan Yuni zuwa Yuli.

Kamar yadda rahoton yazo, "Mun samu labarin yadda aka kama daliban babbar makarantar Loreto da aka dakatar saboda kama su da aka yi suna lalata, duk da ba'a kamasu turmi da tabarya ba.

"Wasu iyayen daliban sun yi ta kiran waya suna rokon ma'aikatar ilimi da ta saka baki akan tsawon lokacin da aka dakatar da daliban. Don haka muka tura masu bincike a ranar Juma'a don jin tabbacin al'amarin. Yanzu haka muna jiran rahoto ne daga wurin su."

KU KARANTA: Zulum ya raba wa iyalai 5,000 kayan abinci, ya ziyarci dakarun soji a Borno

Dumu-dumu: Hukumar makaranta ta kama 'yan aji 4 na sakandare suna lalata a kungiyance
Dumu-dumu: Hukumar makaranta ta kama 'yan aji 4 na sakandare suna lalata a kungiyance. Hoto daga @Lindaikejiblog
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan daba sun kaiwa tawagar gwamnan APC hari (Hotuna da bidiyo)

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya yabi majalisar dinkin duniya akan kokarinta wurin kawo zaman lafiya a Najeriya, musamman a arewa maso gabas.

Yace hakika shigar majalisar cikin al’amarin ya haifar da 'da mai ido. Yace jihar Filato tana fuskantar matsalar rashin tsaro amma tun bayan majalisar ta sa baki al’amura suka fara daidaita.

Gwamnan yace, “A tarihi, jiharmu ce jihar farko da kungiyar ta fara samar wa zaman lafiya.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel