Kamfanonin Lantarki Sun Zalunci Mutum Miliyan 7.1, Sun Ci N105bn a Cikin Watanni 9
- Kamfanonin raba wutan lantarki su kan kawowa mutane takardar kudin wuta a duk karshen wata a Najeriya
- Duk mutumin da bai amfani da na’urar da ke auna yawan shan wuta, zai iya biyn kudin lantarkin da bai gani ba
- A irin haka ne kamfanonin DisCos su ka ci N105bn daga hannun mutane a shekarar 2023 da ta wuce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Kamfanonin da ke da alhakin raba wutan lantarki a Najeriya wadanda aka fi sani da DisCos, suna zaluntar abokan huldarsu.
Wani bincike da aka gudanar ya nuna kamfanonin DisCos sun karbi kudin da ya zarce na hakkokinsu, Punch ta kawo labarin a yau.
Lissafin awon igiyan lantarki
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wuraren da babu na’urar yin awo, DisCos su na amfani da lissafinsu ne wajen karbar kudin wutan da su ka raba a duk wata.
Tsakanin Junairu da Satumban 2023, binciken da aka yi ya nuna kudin da aka karba a hannun mutane miliyan 7.1 ya wuce kima.
Kamfanonin DisCos sun ci banza
Jaridar ta ce a irin wannan lissafi na zalunci kamfanonin DisCos da ke fadin kasar su ka samu N105bn daga Junairu zuwa Satumba.
Kamfanin Yola Disco ya karbi N541.9m daga hannun mutane 42,902, wanda binciken ya nuna wutan da suka sha ba ta kai haka ba.
Abuja Disco kuwa sun ci N17.9bn ta hannun mutane 1,823,218. A Kano, a wajen mutane 71,120 kamfanin wuta ya sau N196.97m.
Kamfanin Benin Disco ya yi zukun N10.5bn wajen karbar kudin wuta daga mutane 754,849 da ke samun lantarki ta karkashinsu.
Shi kuwa kamfanin lantarkin Enugu, ya tatso N11.9bn daga wajen mutane 1,011,402 kamar yadda Jos Disco ya samu har N13.3bn.
A tsawon wannan lokaci, mutane sama da 370, 000 Eko Disco ya yi wa lissafin awon igiya, ya karbe masu abin da ya kai N14.13bn.
Matsalar lantarki a Najeriya
Haka lamarin yake a kamfanonin Ibadan Disco, Ikeja Disco, Kaduna Electric da sauransu, mutane na biyan kudin da ba su sha ba.
Baya ga matsalar rashin wuta a garuruwa, binciken da gwamnati tayi ya nuna adadin wutan da mutane suka sha bai kai haka ba.
Karin albashin ma'aikata
A wani labarin dabam, za a ji Osita Okechukwu ya ce akwai mummunan hadari idan aka tashi mafi karancin albashi sosai a kasar nan.
Jagoran na jam’iyyar APC yake cewa yin karin kudi mara ma’ana zai kara matsalar hauhawar farashi, zai fi kyau a samar da gidaje.
Asali: Legit.ng