An Ji Kunya: Matasa Masu Karfi a Jika Sun Kashe Zuciyarsu, Sun Sace Fanka a Masallaci

An Ji Kunya: Matasa Masu Karfi a Jika Sun Kashe Zuciyarsu, Sun Sace Fanka a Masallaci

  • ‘Yan sanda sun kame wasu matasa da ake zargin sun shiga masallaci sun sace fanka guda bakwai tare da aikata mummunan laifi
  • An kama wani matashi da zargin ya dates hannun dan acaba tare da sace masa babur a wani yankin jihar Neja da Arewacin Najeriya
  • Ba sabon abu bane a yanzu samun yadda ‘yan ta’adda ke aikata munanan laifuka kuma su tsira ba tare da wata tsangwama ba

Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Neja - Rundunar ‘yan sandan ta ce ta samu nasarar cafke wasu barayi da ake zargin sun yi awon gaba da magoya fankoki a wani masallacin Juma’a da ke unguwar Dutsen Kura-Kwasau a garin Minna, babban birnin jihar Neja.

Kara karanta wannan

Bambarakwai: Jerin kasashe 5 da mata ke biyan mazaje sadakin aure

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ya fitar, y ace an kama barayin ne da buhu biyu dauke da fankoki bakwai kuma sun amsa cewa tabbas satowa suka yi.

An kama barayin fankokin masallaci a Neja
Yadda aka kama barayin fankokin masallaci a Neja | Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

Wadanda ake zargin dai sun hada da Mohammed Abdulsamiu dan shekara 21 da Abdulraheem Abdulsamiu dan shekara 16 da Abdullahi Usman dan shekaru 17.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su waye barayin fankan da aka sace a Neja?

AIT ta ruwaito cewa, dukkansu mazauna yankin Dutsen Kura Gwari ne kuma sun yi kaurin suna wajen sata a masallatai da gidajen jama’a.

A cewar ‘yan sanda, an gurfanar da wadanda aka Kaman a gaban kotu don tabbatar da an hukunta su daidai da tanadin dokar kasa.

An kama matasji da laifin dates hannun dan acaba

Hakazalika, jami’an sun kama wani matashi dan shekaru 22 da haihuwa da laifin datse hanun wani dan acaba da ya hau bayansa zuwa wani kauye, Tribune Online ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 13 a Abuja, sun nemi N900m kudin fansa

A cewar DSP Abiodun, wanda ake zargin, Usman Maniya na kauyen Gbete da ke karamar hukumar Mokwa ta jihar, ya hau babur din da fari kafin daga bisani ya yi masa fashinta tare da dates hannunta.

Ta yaya aka kama matashin?

A cewar rundunar ‘yan sandan, jami’anta sun kama wanda ake zargin ne daga yankin Kudu, reshen Mokwa bisa bayanan da suka samu daga al’ummar yankin.

An kwato kayayyakin aikata laifi da suka da adda da kuma babur din da ya kwata daga hannun dan acaban.

Jihohin Arewacin Najeriya na yawan fama da ayyukan ta’addancin ‘yan bindiga da sauran ‘yan ta’addan da ke addabar jama’a.

An kama wadanda suka sace akwatunan zabe a Kano

A wani labarin, 'yan sanda a jihar Kano sun yi nasarar kame wasu gungun mutanen da ake zargin sun sace akwatunan zabe a zaben maye gurbin da aka gudanar na 'yan majalisu.

Kara karanta wannan

Miyagu sun tafka ɓarna, sun yi garkuwa da fasinjojin jirgin ruwa a Najeriya

Matasan da aka kamen an ce suna dauke da muggan makamai, kuma sun nufi tada hankali a zaben da aka yi a karamar hukumar Kunchi ta jihar.

An tattaro cewa, wasu tsagerun matasa 'yan daba sun sace akwatunan zabe a karamar hukumar Tsanyawa duk dai a Kanon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.