Tashin Hankali Yayin da 'Yan Damfara Suka Yi Kutse a Lambar Wayar Gwamnan APC, Sun Fara Neman Kudade
- Jama’a da dama sun kadu bayan kutse da ‘yan damfara suka yi a daya daga cikin lambobin wayar Gwamna Bassey Otu na Cross River
- Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan damfarar tuni suka fara neman taimakon kudade daga jama’a wadanda kaddarar ta fada kansu
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Emmanuel Ogbeche ya fitar a yau Lahadi 11 ga watan Faburairu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Cross River – Gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu ya shiga matsala bayan ‘yan damfara sun yi kutse a lambar wayarsa.
‘Yan damfarar tuni suka fara neman taimakon kudade daga jama’a wadanda kaddarar ta fada kansu, cewar Punch.
Yaushe aka sanar da kutsen a layin gwamnan?
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Emmanuel Ogbeche ya fitar a yau Lahadi 11 ga watan Faburairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Emmanuel ya gargadi jama’a da su yi hankali da ‘yan damfarar inda ya ce su na bin mutane neman taimakon kudade, cewar Vanguard.
A cewar sanarwar:
“Akwai damuwa yayin da ake tura sakwanni ga jama’a da sunan Gwamna Bassey Otu na jihar Cross River.
“Ana gargadin jama’a da su yi hankali da sakwannin da ake turawa da sunan Gwamna Bassey Otu."
Shawarin da aka bai wa mutane
“An yi wa daya daga cikin lambobin wayar gwamnan kutse wanda ake zargin kwararrun ‘yan damfara da aikatawa da safiyar yau Lahadi 11 ga watan Faburairu.”
Ogbeche ya ce damfarar ta sauya salo inda suke neman cutar mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, inda ya ce a yi hankali kada a fada tarkonsu, Osun Defender ta tattaro.
Ya kara da cewa:
“An samu nasarar karbe ikon lambar wayar daga hannunsu yayin da jami’an tsaro suke kokarin binciko tare da kama wadanda ake zargi.”
‘Yan damfara sun yi kutse a banki
Kun ji cewa ‘yan damfara sun yi kutse a bankunan Najeriya yayin da aka tafka asarar naira biliyan daya.
Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da Hukumar NDIC ta fitar inda ta ke fargabar yawan sace-sacen.
Asali: Legit.ng