Budurwa ta maka mahaifiyarta mai shekaru 97 a kotu kan 'kutse' a gidanta na gado

Budurwa ta maka mahaifiyarta mai shekaru 97 a kotu kan 'kutse' a gidanta na gado

  • Wata mata 'yar Kirinyaga mai suna Mary Nguru ta roki kotu da ta dakatar da mahaifiyarta daga shiga, gami da hantarar ma ta 'yan haya a harabar gidanta
  • Nguru ta bayyana yadda gidan da ake rikici a kai yake mallakinta, kuma bata bukatar mahaifiyarta da sauran 'yan uwanta shida da su amfana da wurin
  • Matar ta ce mahaifiyarta, wacce ke amfani da kujerar guragu, na shiga ma ta gida ba tare da izininta ba, gami da cewa 'yan hayanta su daina bata kudin haya
  • Wairimu ta musanta shiga harabar gidan ba tare da izini ba, inda ta tsaya a kan cewa akwai wani bangare da ta gada a gidan da ake rikicin daga marigayin mijinta Cyprian Kimanjul

Kenya - Wata mata 'yar garin dake Kenya ta maka bukaci kotu da ta dakatar da mahaifiyarta, Sabena Wairimu, wacce ke amfani da kujerar guragu daga shiga ma ta harabar gida ko kuma hantarar ma ta 'yan haya, Mwakilishi ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Matar da ta fi kowacce mace kudi a Najeriya ta bukaci mata da su mika wuya ga mazajensu

Mary Nguru ta hakikance a kan cewa ita ce mai gidan, kamar yadda rahoton Nation Afrika ya bayyana, Nguru ta tsaya a kan cewa ita ce mamallakiyar kadarar da ake rigima a kai, sannan ta dade tana biyan kudin wutar lantarki da na ruwa a ofishinsu.

Budurwa ta maka mahaifiyarta mai shekaru 97 a kotu kan 'kutse' a gidanta na gado
Budurwa ta maka mahaifiyarta mai shekaru 97 a kotu kan 'kutse' a gidanta na gado. Hoto daga mwakilishi.com
Asali: UGC

"Zan cigaba da daukar asara da barnar dukiya idan ba'a dakatar da wadanda ke kare kansu ba," a wata takardar da Nguru tayi rantsuwa.

A karar da ta shigar a 2015, Nguru ta tsaya a kan cewa, ta dade tana biyan kudin harajin gidan a alkaryar gwamnatin Kirinyaga.

Nguru ta ce, mahaifiyarta wacce ake kararta tare da sauran 'ya'yanta shida, sun ahiga ma ta gida ba tare da izininta ba, gami da umartar 'yan hayanta da su daina bata kudin haya.

Kara karanta wannan

Katsina: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 2, sun ceto wasu da aka yi garkuwa da su

Haka zalika, wadanda ake karar sun bada takardar dake umarta wasu daga cikin 'yan hayan da su tashi daga gidan, tare da balle wasu daga cikin kofofin bayikan da aka rufe.

Wairimu ta ce ita gaji wani bangaren gidan ne daga marigayin mijinta, amma yayin kare kanta, ta musanta aukawa kadarar wani ba tare da izini ba.

Ta tsaya avkan ta gaji wani bangare ne daga marigayin mijinta Cyprian Kimanjul, sannan ba ta san sanda ta mallaka wani daga cikin kasonta ga 'diyarta ba ko wani daban.

"Zan so in tabbatar da cewa, kadarar da ake rikici a kanta ba mallakin wacce ta shigar da kara bane, sai dai ta fada ne cikin gadon marigayin mijina, duba da za a iya gadon kadarar wanda ya mutu," a cewarta.

Da haka ne aka dage sauraron karar zuwa 11 ga watan Mayu.

Bidiyo: Bayan shekara 20 da batan ta, mahaifiyar yara 8 ta dawo gida da kafafunta

Kara karanta wannan

Bidiyo: Bayan shekara 20 da batan ta, mahaifiyar yara 8 ta dawo gida da kafafunta

A wani labari na daban, wasu 'ya'ya sun tsunduma cikin tsananin farinciki bayan an gano mahaifiyarsu Florence Ikhine, wacce ta bace a shekarar 2002 a Benin dake jihar Edo bayan kwashe shekaru 20 da bacewarta.

Princess Ehima Elema wacce ta sanar a shafinta na Facebook a shekarar 2019 cewa Florence, mahaifiyar yara takwas ta bace, ta sanar da dawowar mahaifiyar 'ya'ya takwas din.

Asali: Legit.ng

Online view pixel